Hakikar Shi'anci



Tohuwar (Tasowar) Shi’anci da Asalinsa

1- Dakta Abdul’aziz Adduri ya kawo asalin Shi’anci da kasa shi kamar haka ne cewa akwai na akida wanda ya fara daga lokacin Annabi (a.s) ne. da kuma na siyasa da ya fara bayan kashe Imam Ali (a.s). Kuma ya kafa dalili a kan haka da cewa ma’anar Shi’anci an yi amfani da ita ne a lokacin "Tahkim" –wato hukunci tsakanin jama’ar Imam Ali (a.s) da ta Mu’awiya dan Abusufyan- wanda a cikin aka ambaci jama’arsu da shi’ar Ali (a.s) da kuma shi’ar Mu’awiya, abin da yake nufin mabiya Ali (a.s) da kuma mabiya Mu’awiya ba tare da kawo wasu abubuwan da suka shafi siyasa ba bayan hakan.

2- Muhammad Farid Wajdi a "Da’iratul ma’arif" ya ce: "Shi'a su ne wadanda suka goya wa Ali (a.s) baya a cikin jagorancinsa kuma suka yi imani da cewa jagoranci ba ya fita daga â€کya’yansa, kuma suka yi imani da ismar imamai daga zunubbai manya da kanana, da kuma yin imani da wilaya da bara’a (wato kauna da biyayya da kuma barranta) a zance da aiki, sai dai a lokacin takiyya idan sun ji tsoron azzalumi kuma sun kasu kashi biyar; â€کKaisaniyya, Zaidiyya, Imamiyya, Gullat, da Isma’iliyya’ kuma wasunsu suna karkata zuwa ga Mu’utazilanci wasu kuma zuwa ga Sunna, wasu kuma zuwa ga Tashbihi".

 wannan bayani na Farid Wajdi ya rigaya cewa na kawo wani bangare nasa a bayanin ma’anar Shi’anci kuma na kawo wannan ne domin in kawo shi gaba daya, domin bayanin abin da ake fada kan Shi’anci tun farkonsa har zuwa yau, domin mu sani cewa wadannan kalmomi ba a rana daya ba ne aka shigar da su cikin ma’anar Shi’anci, sannan kuma mu iya gani afili cewa Farid Wajdi ya hada wani cakude kawai ya sanya abin da ba Shi’anci ba cikin Shi’anci kuma ya jingina wa Shi'a abin da su sun barranta daga gareshi, kuma ni ba na son in gaggauta raddi ne gare shi sai ya kasance tun yanzu mun shagaltu da irin wadannan jawabai da raddinsu a wurin da ya dace da su a wannan littafin.

3- Dakata Kamil Mustapha a littafinsa na "Assila" ya ce: "Bayan haka yana bayyana garemu cewa Shi’anci ya faro tun farkon musulunci a matsayinsa na kashin bayansa, kuma ya bayyana kamar wata kungiya ta siyasa bayan Mu’awiya ya yi gaba da Imam Ali (a.s) a game da jagorancin al’amuran musulmi, sai ya bayyana bayan haka a matsayin wani motsin gwagwarmaya mai karfi karkashin Sunan Shi’anci bayan kashe Imam Husain (a.s) kai tsaye, don haka muna iya cewa Shi’anci wani abu ne da ya bayyana tun lokacin Annabi amma ya karfafa a mtasyin siyasa bayan kashe Usman dan Affan sannan sai ya kasance kalma ce da ake amfani da ita a isdilahinta bayan kashe Imam Husaini (a.s). kuma wannan yana nufin ya bi marhaloli daban-daban domin ya samu kamalarsa kamar yadda Dakta Kamil yake cewa.

 4- Dakta Ahmad Amin ya ce: "Shi’anci ya fara tun farko da ma’ana mai sauki wato cewa Ali (a.s) shi ne ya fi waninsa ta fuska biyu: Shi kansa da kuma kusancinsa da Annabi (s.a.w). Sai dai wannan Shi’anci ya dauki wata sabuwar sura da sabon salo da aka shigar da wasu sababbin abubuwa a cikin addinin musulunci wadanda suka hada da yahudanci da kiristanci da majusanci. Kuma tunda mafi girman abin da aka shigar a musulunci daga Farisawa ne, to don haka ne ma suke da gudummuwa mafi yawa a tasiri kan Shi’anci.

A fili yake cewa daga abin da Ahmad Amin ya fada muna iya cewa shi a ra’ayinsa ke nan Shi’anci ya samu daukaka da ci gaba ne ba don wani abu da ya tofo daga cikinsa ba, sai dai saboda kare-kare da aka yi wa addinin musulunci da akidojin wasu addinai da aka sanya akidojinsu a musulunci, sannan kuma sai Shi’anci ya zabe su daga musulunci ya kuma karbe su suka zamanto wani bangare nasa, har sai da ya kasance yadda yake. Kuma yana ganin cewa Farisawa sun yi tasiri ke nan kan wannan mazhaba fiye da waninsu kamar yadda shi Ahmad Amin yake son nunawa. Kuma wannan ra’ayi ne da Ahmad Amin ya samu daga waninsa kuma shi ma waninsa ya samu daga wani ne har dai a kai ga mutum na karshe na farko da ya fara yin wannan maganar kage kan Shi'a, har dai wannan maganar ta kusan zama wani dalili gun wasu masu bincike masana. Kuma in Allah ya so nan gaba kadan zan nuna maka karyar wannan kage da kuma hadafin da ake son cimma da wadannan maganganu na damfara Shi’anci da Farisanci.

5- Dakta Ahmad Mahmud Subhi ya ce:

"Bayan ya kawo abubuwan da aka fada kan Shi’anci da kuma kawo cewa dangantakar Shi’anci ga Shi'a kamar zuhudu ne lokacin manzon Allah (s.a.w) da halifofin farko, da kuma bambancinsa da sufanci da ya wakana a lokacin ganusiyya da kuma tasirantuwarsa da wasu fikirori da akidu masu sabawa da juna kamar yadda aka sani gun muhyiddin Ibn Arabi da kuma Sahrawardi a misali".

Bayan duk wadannan misalai da maganganun da suka zo daga wasu litttattafai da suka kawo bambancin Shi’anci a farkon musulunci da kuma zamunan da suka biyo baya sai ya rufe magana da wadannan bayanai masu zuwa da cewa:

1- Adadin mas’alolin tunani na Shi'a suna dada yawa fiye da yadda suke a zamanin farko babu wani kokwanto, wanan kuma ba domin daduwar asalin asasin fikirar Shi’anci ba ne, sai dai domin yawaitar karin bayanai dalla-dalla da sharhin dunkulallun bayanansa, ba wai dadi ba ne kan asasin abin da ya kafu a kansa, sai dai bayanin asalin Shi’anci ne, kuma wadannan bayanai suna bayyana dalla-dalla a tsawon zamuna da suka gabata har zuwa yau.



back 1 2 3 4 5 6 next