Aure Mai IyakaA littafin Tamhid, na Ibn Abdulbarr, yana cewa: malamai sun hadu a kan cewa auren mutu'a babu shaidu a cikinsa, kuma shi aure ne zuwa wani lokaci, kuma rabuwa a cikinsa tana kasancewa ba tare da saki ba, kuma babu gado tsakaninsu[16]. Asalin Sabani Kan Auern Mutu'a
Bisa ga abubuwan da suka faru, idan muka duba zamu ga sabanin da ake da shi game da auren mutu'a ya taso ne sakamakon shafe hukuncinsa da haramta shi da ya faru a lokacin halifancin Umar dan Khaddabi. Domin idan mun duba zamu ga halaccinsa lokacin Manzo (s.a.w) da kuma lokacin halifa na farko, da wani bangare na rayuwar halifancin halifa na biyu, har sai da halifa na biyu ya fadi mash'huriyar kalmarsa da yake cewa: "Mutu'a biyu (wato auren mutu'a da hajjin tamattu'i) sun kasance a lokacin Annabi (s.a.w) amma ni na hana su, kuma zan yi ukuba (ladabi) a kan yin su"[17]. Malamai gaba dayansu sun tafi a kan cewa a fili yake haramcin ya zo daga halifa na biyu, a karshen kwanakin halifancinsa, wannan kuma shi ne abin da Ada' yake kara karfafawa, cewa muna yin auren mutu'a a lokacin Manzo (s.a.w) da Abubakar, da Umar, har sai da ya kasance a kwanakin karshe na halifancin Umar, sai Amru dan Haris (ko Hurais) ya yi mutu'a da wata mata da Jabir ya gaya mini sunanta amma na manta, sai matar ta yi ciki, sai labarin ya je ga Umar, sai Umar ya hana yin auren mutu'a[18]. Wannan haramcin ya zo a littattafai masu yawa, sannan kuma da kausasawa kan wanda ya saba masa, ta yadda ana iya jefe koda kuwa kabarinsa ne bayan mutuwarsa. Sannan kuma Umar ya hana auren ne a kusan karshen rayuwarsa; Duba: Almusannif na Abdurrazak bn Hammam: 7/467, da Muslim sharhin Nawawi: 6/127, da Masnad Ahmad: 3/304, da Sunanul Kubura: 7/237. Ya ci gaba da cewa, amma wannan haramcin ba haramci ba ne karami, ba haramci ba ne kamar sauran haramci, domin shi haramci ne na ladabi da ukuba, kuma haramci ne tare da tsoratarwa da jifa. Ku duba ku gani yana cewa: Da labari ya zo mini cewa wani mutum ya yi shi, sannan kuma ya riga ya mutu, da na jefe kabarinsa[19]. Umar dan Khaddabi yana cewa: Da labari ya zo mini wani mutum ya yi auren mutu'a da wata mata, koda kuwa na same shi ya riga ya mutu to sai na jefe kabarinsa[20]. Wannan haramcin yana nuna mana cewa kafin lokacin halifa na biyu babu shi, bai zo ba sai daga Umar dan Khaddabi. Wani mutumin Sham (Siriya) ya kasance ya zo sai ya auri wata mata auren mutu'a, sannan sai ya fita daga gari, sai Umar ya ji labari ya sa aka kamo shi. Sai ya ce da shi: Me ya sa ka yi? Sai ya ce: Mun kasance muna yi lokacin Manzo (s.a.w) bai hana ba har Allah ya karbi ransa, da kuma lokacin Abubakar shi ma bai hana ba har Allah ya karbi ransa, sannan muna yi a lokacinka ba ka hana shi ba. Sai Umar ya ce: Na rantse da Allah da na riga na hana yin sa, sannan sai ka yi shi, da na jefe ka![21]. Wannan yana nuna har zuwa wannan zamanin babu wannan hanin, don haka daga nan ne wannan hanin ya faru. Don haka ne zamu ga imam Ali (a.s) yana cewa: Ba domin Umar ya hana mutu'a ba, ba wanda zai yi zina sai tababbe[22]. (ba wanda zai yi zina sai ya tabe ya tsiyata). Kuma dukkan malamai sun danganta haramcin zuwa ga Umar ne.
|