Aure Mai IyakaA nan sai mu ce; Shi dai aure kowane iri ne ganin dama ne, sannan abin da ya sanya mu kare wannan aure shi ne: Kasancewarsa shari'ar manzon Allah (s.a.w) ce wanda ya zo da addini cikakke daga Allah, da ba shi da wata tawaya balle a yi ragi ko a yi kari a cikinsa. Sannan kuma duk wata maslaha ta dan Adam tana cikin koyi da abin da Annabi ya zo da shi kai tsaye ba tare da wani jayayya ko neman sauyi daga gareshi ba. Menen Auren Mutu'a?
Auren mutu'a shi ne mace mai cikakken hankali, 'ya, ko baiwa bisa izinin Ubangijinta, haka nan budurwa bisa izinin Uba ko Kaka na wajen Uba, ta yi aure da wani mutum zuwa wani lokaci ayyananne, da wani lafazi na musamman da shari'a ta sanya, a kan wani sadaki da aka ambata, da sauran sharuddan da suka zo a littattafan fikihu dalla-dalla. Kuma dukkan sharuddan aure da'imi suna cikin auren mutu'a, sai dai a wasu abubuwan kamar gado idan ba an shardanta shi ba, kuma idan aka mance ba a ambaci mudda ba, to ya koma na da'imi. Sharuddansa
Don haka dole ne auren ya cika sharudda kamar: 1. Yardar bangaren biyu, wato namiji da mace 2. Sadaki: wannan hakki ne na mace, ba ya saraya sai da yardarta ko ta yafe 3. Ambaton muddarsa, ko da kuwa awa daya ce, ko shekara goma, ko makamancin hakan 4. Kada wani abu ya hana kamar dangantaka ta jini ko ta shayarwa, ko ta auratayya da sauran abubuwan da sukan haramta auren mace Bambancinsa Da Na Da'imi
Bambancin auren mutu'a da na da'imi sun hada da: · Na mutu'a yana da lokacin ayyananne da zai kare · A mutu'a ba saki sai dai a yafe ragowar mudda komai yawanta kuwa, ko kuma idan mudda ta kare
|