Aure Mai Iyaka



Don haka muna iya ganin wanda aka ruwaito ya halatta ta a ruwayar da aka kirkira wa manzon Allah (s.a.w) Zuhuri ne, shi kuwa Zuhuri malamin fadar Banu Umayya ne, kuma Imam Sajjad (a.s) ya yi masa nasiha kan abubuwan da yake yi na halatta musu abin da suke so, da haramta abin da ba sa so, amma wasikarsa ba ta yi wa Zuhuri tasiri ba. Wannan wasikar tana nan hatta da Gazali mai littafin Ihya’u Ulumuddin 2/143, ya kawo ta. Sannan kuma Zuhuri ya kasance mai tsananin saba wa imam Ali (a.s) ne, ya kasance mutum ne wanda yake kirkiro hadisai yana jingina wa Ahlul Baiti (a.s), har ma ya kirkiro cewa; Abubakar da Umar ne suka yi wa Sayyida Fadima (a.s) salla, haka nan idan ya tashi kirkirar kage sai ya jingina wa Ahlul Baiti (a.s).

Sannan muna iya ganin yadda malamai daga tabi’ai masu yawa suka yi wannan auren, muna ganin yadda Abdulmalik dan Abdulaziz dan Juraij, wanda ya mutu a shekara ta 149 H, wanda yake daga manyan tabi’ai, kuma daga malaman fikihu, da hadisi, daga malaman Sihah assitta, wannan mutumin ya auri sama da mata casa’in auren mutu’a, kuma ya yi wa ‘ya’yansa wasiyya da kada su auri wasu matan saboda matan babansu ne, muna iya duba Siyaru A’alamun Nubula: 6/333, da sauran littattafai.

Kamar yadda ya zo cewa; Yahaya dan Aksam yana cewa da wani shehin Basara: Da wa ka yi koyi a auren mutu’a? sai ya ce: Da Umar dan Khaddabi. Sai ya ce: Yaya haka, alhalin ka san cewa shi ne ya fi kowa tsakanin kiyayya da ita a cikin mutane? Sai ya ce: Saboda labari ingantacce ya zo cewa; ya hau kan mimbari, sai ya ce: Hakika Allah da manzonsa suna halatta mutu’a biyu (wato; auren mutu'a, da hajjin tamattu'i) kuma ni ina haramta su, kuma ina yin ukuba a kansu, sai muka karbi shedarsa, ba mu karbi haramcinsa ba. Muhadhatul Udaba’: 2/214, na Ragib Isfahani.

Haka nan Yahaya dan Aksam ya hana Ma’amun Abbasi (sarkin Abbasawa) shelanta halaccin auren mutu’a da da’awar cewa; Zai sanya fitina cikin al’umma, yayin da Ma’amun ya soki Umar dan Khaddabi a kan soke hukuncin Allah da manzonsa a shari’a, bai gushe ba har sai da ya yi galaba kan Ma’amun da kada ya shelanta hakan. Wafayatul A’ayan: 5 / 197.

Da wannan ne zamu ga cewa; Auren mutu'a yana nan a halaccinsa daram, kuma babu wani wanda Allah (s.w.t) ya yi umarnin karbar umarni da haninsa, ba tare da raddi ba, sai manzon Allah (s.a.w), don haka muna iya ganin cewa; wadanda suka haramta auren mutu'a, sun yi riko da umarnin Umar ne, wadanda kuwa suka halatta, sun yi riko da umarnin Allah da manzonsa ne!.

Don haka ne Shi'a a matsayinsu na masu biyayya ga kawai abin da manzon Allah (s.a.w) ya zo da shi, da raddin duk wani abu ko daga wa yake kuwa, sun yi riko da wannan halaccin na Allah da manzonsa (s.a.w) har abada.

Auren mutu'a shi ne abin da Ahlul Baiti (a.s) ba su taba yin boyon halaccinsa ba a cikin umarnin Allah da manzonsa a kowane hali, ba su taba kuma yin takiyya a kansa ba. Domin neman albarkar masu albarka, imaman shiriya da rahama, bari mu kawo tattaunawar Imam Muhammad Bakir (a.s) wasiyyin manzon Allah (s.a.w) na biyar, wato halifansa na biyar cikin alayensa Ahlul Baiti (a.s), mu ga yadda ta kasance da shi da wani mutum Allaisi wanda ba ya daga cikin mabiya tafarkinsu. Ga muhawarar kamar yadda ta zo a ruwaya:

Al’abi ya ce: A cikin littafin Nasruddurar: An rawaito daga Abdullahi dan Mu’ammar Allaisi ya ce da Abi Ja’afar (a.s): Labari ya zo mini cewa kai kana bayar da fatawa da yin auren mutu’a? sai Imam Bakir (a.s) ya ce: Allah ya halatta a littafinsa kuma Manzon Allah (s.aw) ya sunnanta, sannan sahabbansa sun yi aiki da ita, sai Abdullah ya ce: Ai Umar ya hana yin ta. Sai Imam Bakir (a.s) ya ce: Kai kana kan maganar sahibinka (Umar), ni kuma ina kan maganar Manzon Allah (s.a.w). Sai Abdullah ya ce: Shin zai faranta maka rai (‘ya’yan) matanka su aikata haka? Sai Abu Ja’afar (Imam Bakir) (a.s) ya ce: Kai wawa? Wannan da ya halatta a littafinsa, kuma ya halatta ga bayinsa ya fi ka kishi, da kai da wanda ya hana, yana mai dora wa kansa nauyi, a yanzu zai faranta maka rai cewa ‘yarka tana karkashin auren wani masaki daga masakan garin Yasrib (Madina)? Sai ya ce: A’a. Sai Imam Muhammad Bakir (a.s) ya ce: Me yasa kake haramta abin da Allah ya halatta? Sai ya ce: Ba na haramtawa, amma dai masaki ba tsarana ba ne. Sai ya ce: Ai hakika Allah ya yarda da aikinsa ya so shi, ya aura masa Hurul-i’n, a yanzu kana kin wanda Allah yake son sa? Kana kin wanda yake tsara na Hurul-i’n din aljanna saboda shisshigi da girman kai? Sai Abdullah ya yi dariya ya ce: Wallahi ba na ganin kirazanku (zukatanku) sai mabubbugar ilimi, sai ‘ya’yan itacensa suka zama a hannunku, ganye kuwa ya rage a hannun mutane[31].

Muna ganin yadda Abu Ja'afar Imam Muhammad Bakir (a.s) ya yi magana kan auren mutu'a da halaccinta, da kuma cewa; a aure babu bambanci tsakanin ma'abota sana'o'i ko kabilu. Yana mai kawar da jahiliyyar da aka raya a cikin musulunci bayan wafatin manzon Allah (s.a.w) ta nuna fifiko tsakanin mutane da kabilu kan aure, da albashi, da sauransu.

 

Bayanan Ciki

Aure Mai Iyaka (Auren Jin Dadi) 3



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next