Tarbiyyar Yara A MusulunciTsakanin Yaro Da ‘Yan’uwansa
Kada ka nuna wa yaronka a fili kafi son daya a cikinsu[14], a nan da mata da yara duka daya ne, soyayyar da kafi yi wa daya kada ta zama a fili, koda zaka yi wa daya wani alheri ba ka yi wa sauran ba, to ya zama bisa wani abu da yake yi su ba sa yi, kuma da ma can ka yi alkawari duk wanda ya kiyaye zaka taimaka masa, kamar ka saya masa abin hawa don yana zuwa makaranta kuma duk wanda yake zuwa to shi ma za a saya masa don yana zuwa makaranta ne. Tarihin Annabi Yusuf (A.S) shi da babansa (A.S) da wahalar da suka sha ya isa darasi, wannan ba don ya zama laifinsu ba ne, sai don Allah ya fifita shi a kan ‘yanuwansa ne, don haka ne ma da ya yi mafarki duk da baban ya umarce da ya boye amma da suka ga ya fi su karbuwa wajan Allah da al’umma Sai suka kulla makirci su kashe shi amma Allah ya tseratar da Annabinsa Yusuf (A.S). Abin haushi da aka samu wasu maganganu raunana a tarihi da aka jingina su ga Annabin Allah Ya’akub (A.S) wannan duka badili ne da aka jingina ga Annabi Ya’akub (A.S), Annabi Ya’akubu (A.S) Ma’asumi ne. Da akwai nau’i na soyayya da a kan kebanci yara da shi wanda su kan su manya babu wani abu da sukan ji don an ba wa yara irin ta, irin wannan ne Annabi Ya’akubu (A.S) ya bai wa Yusuf da dan’uwansa Bunyamin, sannan akwai fifiko da kebanta da zabi daga Allah gare shi wanda bai buya ga kowa ba[15]. A sanadiyyar wannan son ne ‘yan’uwan Annabi Yusuf (A.S) suka Wasu Hanyoyin Tarbiyya Yara
Wasu daga cikin hanyoyin tarbiyyar yara wadanda aka jarraba su, su ne kamar haka: Na daya: Ta hanyar bayar da labarai da kissoshi, misali na san mahaifinmu ya taba ba mu labari kan hadarin wulakanta mutane domin ba ka sani ba ko wani waliyyi ne ka wulakanta sai Allah (S.W.T) ya yi maka azaba, wannan kuwa ba na mantawa a shekarar 1983 ne, sai ya zamanto idan mun ga wani yana tsokanar wani mutum saboda tawaya ta halittarsa mukan gaya masa ba ka sani ba ko waliyyi ne. Yaro mutum ne mai son tarihi da labarai kuma a lokacin da nake koyarwa a Furamare da kuma Sakandare na ga amfanin haka sosai da yadda soyayya da kaunar juna ta faru tsakanina da dalibai, har ma koda a Wasu marasa fahimta daga malamai sukan samu tsangwama daga dalibai musamman ma wanda ya zama mai bulala, an ce lokacin da turawan yamma suka zo kasashenmu a makaranta sai a ba wa malamin ilimin Addini ya zama shi ne mai duka sai duk dalibai ka ga suna kin malamin da ma darasin nasa, shi kuma yana daure fuska da barazana ga dalibai wai shi ne mai bulala. Da haka ne sai yara su nisanci darasi na Addini su gan shi a matsayin wani ci baya ne kuma ba abin da ma’abotansa suka sani sai su yi bulala ga dalibai. Ta hanyar labaru kakan iya koyawa yara jarumtaka da girmama mutane, da son al’ummarsu, da neman kawo gyara cikinta, da jin lallai dole su dauki nauyin isar da sakon Allah ga mutanensu, da son kyauta da taimakawa marasa shi, da nisantar rowa, da sadaukarwa don mutanensu, da son iyaye da rashin saba musu, da kaskantar da kai ga mutane, da sanin Allah da girmansa da tsoronsa. Na biyu: Abokantaka da danka ta yadda zaka iya yi masa tasiri ta hanyar hira da shi da nuna masa shi ma mutum ne, kuma yana iya tunani har ma ka dauki shawara daga gare shi ta yadda zai ji cewa shi ma mutum ne kamili. Rashin wannan ya sanya yara suna jin su tauyayyu ne kamar yadda aka tarbiyyatar da mata har wannan ya yi tasiri a tunaninsu, haka ma aka yi wa yara irin wannan mu’amala har ya yi musu tasiri, shi ya sa saudayawa sukan taso ba su san al’ummarsu ko duniyar da suke cikinta ba.
|