Tarbiyyar Yara A Musulunci6- ‘Ya’yan da ba na kirki ba, ba su da wani amfani a lahira: Mumtahannat: 3. 7- Kada ‘ya’ya su hana tuna Allah: Munafikun: 9. 8- Wasu ‘ya’yan nutsuwar rai ne kuma sanyin idanuwa ga mutum: Furkan: 74. 9- Yi wa ‘ya’ya wa’azi da nasiha: Lukman: 13. 10- Yi wa ‘ya’ya addu’a ta gari: Ibrahim: 35. 11- Yi wa ‘ya’ya nasiha da wasiyya a karshen rayuwar iyaye kafin mutuwarsu: Bakara: 132[2]. Yaro Aboki Ne Garemu
Ya zama wajibi na farko a kan mutanen gida kamar uwa da uba su kusanci ‘ya’yansu, su zama abokansu a gida domin samun damar ba su tarbiyya, wasu mutane sun dauki ‘ya’yansu kamar abokan gaba ne. Misali; wata rana na ga wani mutum da yake cin abinci da abokansa suna hira, yana waiwaya bayansa sai ya ga dansa[3] sai ya kwada masa mari, sai da ya mike tsaye ya sake faduwa har sau biyu, sai kara masa yake yana cewa: Wato Muhammadu da kai ne a nan! Abin haushi da abokan suka zura masa ido kamar suna ganin abin da ya yi daidai ne, ba su ce masa uffam ba. Haka nan wasu suka dauka kamar yaronsu ba mutum ba ne, ba a magana da shi ta kirki, ba a yawo da shi, ba a ma kula shi, ana ganin sa kamar ba mutum cikakke ba, wasu ma suna haramta masa soyayyar da yaro yake bukata ga uba, shi ya sa idan yaro ya rasa soyayyar da ake samu daga uba da uwa sai wannan ya sanya shi yin nesa da su, sai ya samu miyagun samari ko wasu ‘yan iska da zasu nuna masa kauna a waje da jin shi mutum ne, yana jin dadin hira da su, yana ganin yana samun wata kariya daga gare su, kuma yana jin shi mutum ne a wajansu, sai ya makale musu su zama abokansa ko ya zama yaronsu, ta haka ne da yawa yara da suka rasa soyayya ta iyaye aka tura su suka zama fasikai ko mabarnata a cikin al’ummarsu. Kamar yadda idan mutanen gida suka nisanci yaro sukan tura shi waje a aikace domin ya samu inda zai samu wannan soyayyar da ya rasa a gida da
|