Tarbiyyar Yara A Musulunci
Aiken Yara A Lokacin Da Ya Dace
Game da aiken yaro yana da kyau a kiyaye lokacin yaro da lokacin da ya kamata a aike shi, misali kada a aiki yaro lokacin da zai tafi makaranta wannan yana iya sanya shi ya ji ba ya son zuwa aiken, kuma shi babba ya kamata ya fahimci cewa yaro yana da nasa hakki kuma babu wani abu da ya kai makarantarsa muhimmanci.
Kada a aiki yaro idan ya gaji, saboda haka idan yaro ya gaji a bar shi ya huta, kamar idan ya dawo daga makaranta a gajiye ko daga wani aike da ya gaji, a nan sai a ce da shi tafi ka huta sannan in aike ka waje kaza, wannan yana sanya yaro ya ji dadin zuwa aike na gaba.
Kada a ba wa yaro aike na babba, domin wannan yana iya sanya shi ya yi kuskure, kuma idan abu wanda yake da nauyi ne ya fi karfinsa kada a ba wa yaron wannan aiken, haka ma idan yara suna da yawa kada a rika aiken daya kawai kamar yara uku ne kuma aike shida ne to ya kamata ne a aiki kowanne aike biyu domin ya zama ba a karya zuciyar daya daga cikinsu ba da takura masa da aike shi kadai, ko kuma a raba musu kwanaki shida ta yadda kowanne yana da kwanaki biyu na aike ya kuma zama daidai maslahar yaro da su masu aiken nasa a cikin gida.
Aiken yaro har ya gaji ko a lokacin makaranta ba shi da kyau shi ya sa mutanen gida kullum idan suna da aike da zasu yi wa yaro to ya kamata ne ya zama bisa tsari da sanin kayyadaddun aike da za a yi masa a rannan.
Godiya Ga Mai Kula Da Yaronka
Yana daga cikin hikima ka rika godiya ga mai kawo maka labarin yaronka ko yi masa tarbiyya, domin hakan zai iya sanya shi ya karfafu wajan taya ka kula da yaronka da tarbiyyatar da shi. Kuma kada uwaye su dauka su kadai sun isa wajan tarbiyyar yaro wannan kuskure ne, don haka idan an kawo maganar yaronka ka ba ta muhimmanci. Amma kana iya bincikawa ka ji gaskiyar lamari wannan babu laifi a ciki musamman idan kana da kokwanto a kai, kuma ka ba wa maganar muhimmanci, kuma ka gode wa mai kawo maka ita, sannan shi kuma yaron ka nuna masa kana sane da abin da yake aikatawa kuma ka dauki mataki a kai, in ba haka ba zai zama ka karfafa shi ya ci gaba, domin yakan iya cewa da su: Ku fada din me za a yi min? kuma wannan yana iya kai wa ga lalacewarsa.
Mutum ko yaya yake kada a yi sakaci wajan tarbiyyarsa domin ta yiwu idan ya girma shi ne zai iya kawo canji ga al’umma, kuma a sani cewa ta sanadiyyar mutum daya ne duk muka zo duniya saboda haka duk mutum yana da kima da muhimmanci.
Mu sani gyara mutum daya a gida gyara gida ne, gyara gida daya shi ne gyara gari, gyara gari daya shi ne gyara jaha, shi kuma gyara jaha gyara kasa ne, gyara kasa gyara ne ga nahiya, wannan kuma shi ne gyara duniya.
Da kowane gida a Duniya ya zama salihin gida da wannan yana nufin Duniya ta zama saliha gaba daya don haka gyara mutum daya shi ne gyara duniya gaba daya don haka bai kamata ba a rika kallon yaro kamar mutum daya ne domin ba a sani ba me zai zama a cikin al’umma da irin canjin da zai iya kawowa a cikinta, shi ya sa masu hikima sukan ce: Mace saliha tsiran al’umma.
Yaro dan Koyi Ne
Yaro dan koyi ne saboda haka tarbiyyarsa a aikace ta fi karfi da tasiri kamar yadda muka gabatar a baya, da yarinya zata ga kullun mahaifiyarta tana fada da babanta to tayiwu idan ta je gidan miji abin da zata yi kenan, don haka a guji duk wani mummunan aiki a gaban yara.
A nisanci karya da wulakanta mutane, da gulma, da zagi, da sauransu, a dasa karatun Kur’ani a gida, da karatu, da labaru na bayin Allah, da gaskiya, da rikon amana, da sallama idan an shigo gida, da godiya ga mutane in sun kyautata, da girmama su, ta haka ne yaro zai iya daukar kyawawan dabi’u a aikace.
|