Tarbiyyar Yara A Musulunci



Tarbiyyar Yara Sai Kowa Ya Sa Hannu

Kakan samu yaro ya yi laifi sai makwabci ya tsawata masa maimakon Uba ya kamo hannunsa wajan makwabcin ya yi godiya a gaban yaron kuma ya nuna wa makwabci in ya sake a ci gaba da tsawatawa sai ya yi fada da makwabcin nasa, da haka sai ya rasa mai kula da halin yaron a waje, shi ya fita kasuwa ko aiki yaro ya fita waje, Uwa ba ta ganin me yake yi Uba ma haka, sai ya yi ta aikata halin banza ko ya bi mutanen banza, makwabta kuma don gudun sharrin uban sai su yi shiru.

Akwai misalin irin wannan da wani mutum da dansa kan jawo mashin din mutane ana tsawata masa amma sai uban ya zo yana cewa: Ina ruwansu ya ma mutu mana! Kada a takura wa dansa! Haka ma a kan samu uwa ta yi irin wannan hali sai makwabta su kyale danta ya lalace, maimakon su iyaye su gane cewa tarbiyyar yara tana bukatar kowa ya sa hannu, da makwbata, da hukuma, da abokai na gari, da ‘yan’uwa, da ma mutanen garinsu, amma su suna ganin kamar su kadai ne zasu iya, ta haka sai su cutar da yaron da al’ummarsa ta hanyar bata rayuwarsa da ba shi mummunar tarbiyya.

Tsoro Da Sakamakonsa Da Marhalarsa

Tsoro wani hali ne da yake daga dabi’ar mutum, yakan iya karuwa ko raguwa ta hanyoyi daban-daban, ga yaro tsoro wani abu ne da yana iya tasowa da shi, yarinta abu ne mai cike da tsoro musamman saboda yara suna cike da jahiltar abubuwa da dama wadanda a bisa dabi’arsu yana iya tsorata su ko ya kayatar da su. Haka ma rashin sabo yakan sanya tsoron wani abu wanda da ya zama sananne gare shi da ba ya iya tsorata shi.

Mutumin da yake tashi a matsoraci ba ya iya amfanar al’ummarsa matukar ba an yi maganin tsoron ba, kuma ba ya iya kawo mata canji, wannan kuwa ko ta hanyar gyara a cikin al’ummarsa kamar Salihi irin Shehu dan Fodio (R.A) ko mutumin da yake mujrimi babba a Duniya kamar Hetla da makamantansa, sabaoda haka ne ake son yaro ya tashi da kwazo da jarumtaka da juriya.

Tsoro yakan sa mutum ya fita daga halinsa na dabi’a har ya yi galaba a kan iradarsa da azamarsa ya zama mutum mai rashin kuzari da rauni har ma yana iya rasa karfin aikata wani abu. Saboda haka yana daga mummunan abu ba wa yara labari da tatsuniyoyi na ban tsoro da sukan iya rusa musu irada da niyya da azama, wani lokaci saudayawa uwa domin tana son yaro ya yi shiru sai ta ba yaro tsoro kamar ga mage nan ko ga sunan.

Tsoro ga yaro ya dan bambanta ga tsoro gun manya don tsoronsa bai doru bisa dalili na hankali ba, misali yaro yana tsoron duhu shi ya sa bai dace ba a yi bacci tare da yaro sai kuma uwa ta tashi ta barshi a cikin duhu, wannan yana iya sa yaro ya tashi a gigice har ma yana iya fadawa kan wani abu da kan iya yi masa lahani. Saboda haka tsorata yaro kan iya sanya shi cikin wani hali da yakan iya rusa masa nufi da azama, amma tsoro kamar na talauci irin wannan yana tasowa daga tunani ne wannan yana samun manya ne.

Haka ma yaro kan ji tsoron wanda bai sani ba sai dai idan ya saba da shi, shi ya sa idan zaka je wani gida don ganin kananan yaran ‘yan’uwanka da ba su sanka ba, kuma kana so su saba da kai a nan sai ka kai musu wani abu kamar kayan wasanni da wasu abubuwa da yara suke so kuma ka yi musu wasa da su, a lokacin ne zaka ga sun kawar da wani tunani na bakunta da suke game da kai na tsoron wanda ba su sani ba daga kwakwalensu ko kuma ya ragu sosai.

Ana cewa: Idan yaro ya kai wata shida yakan fara tsoro haka idan ya kai shekara daya yakan fara tsoron dabbobi kamar mage da bera, a shekara ta biyu yakan ji tsoron komai kamar kare da mota da sauransu.

Sababin Tsoro Da Maganinsa

Saudayawa yaro yakan fara jin tsoro na wani abu a sakamakon ya ga iyaye mata suna jin tsoronsa ne kamar kyankyaso, ko tsawa, ko wani abu da a kan shuna masa shi wanda muka riga muka ce irin haka babu kyau ko kadan. Haka nan kada a bar shi cikin kadaita ko ya ga manya suna fada. Abin da ya kamata a tsoratar da yaro daga gare shi, shi ne abin da aka san yana cutar da shi, kamar nisantar rijiya, ko wuta, ko wani abu da cinsa yakan cutar da shi, duk da abin da ya fi shi ne nisanta su daga gare shi, ba kawai nisantar da shi daga gare su ba.

Da zaka ga yaronka ya taso da tsoro maras dalili to ya kamata ne kasan menene mafarinsa don kasan yaya za a yi maganinsa, misali idan ya taso matsoraci saboda miyagun tatsuniyoyi na ban tsoro da yake ji ne to sai a koma a sanya musu lokaci na labarai na mazaje masu jarumtaka da sadaukarwa da sauransu har ma ya yi masa tasiri, amma tare da kiyayewar cewa abin da su jarumai suka yi abu ne na alheri da bai saba wa koyarwar musulunci ba, Sa’annan iyaye yana da kyau su saba wa yaro da suna iya barinsa shi kadai a dakinsa ya kwana kuma wannan ba komai ne ba domin ya saba da zama da kafafunsa a abubuwa da dama da jarumtaka.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next