Hakkoki A MusulunciHaka nan yana kan mai sayan kaya ya girmama mai sayarwa shi ma mai sayarwa ya mutunta mai saya, likita da marasa lafiya, mai kudi da talaka, malami da marasa sani, mai haya da dan haya, mai aiki da shugaba. Bai kamata ba shugaba a ma’aikata ya rika kallon masinja kallon wulakanci, hakki ne a kansa ya girmama masinja, ya tuna shi ma dan kasa ne kamarsa kuma ma’aikaci da bai fi shi da komai ba a wajan Allah sai dai idan ya fi shi takawa domin ita ce ma’aunin fifiko. Haka ma dan hayar mota kamar Taksi da Bos (hayis) kada ya zama idan ya ga fasinja yana ganin naira goma ne ko biyar ko ishirin, hakki ne a kansa ya ga mutum yake kallo kafin ya ga Naira ishirin, kuma ya yi mu’amala da shi ta mutunci da girmamawa tsakanin juna. Haka nan alakar na kan mota da na kan jaki, da na jirgin sama da na kasa[33], duka daya ne a wajan Allah kuma ba mai fifiko sai da takawa, rashin kiyaye wannan da mantawa da Allah ya sanya rashin kiyaye hakkin juna. Wani misali a kan haka shi ne; wata rana wani mai kudi shahararre ya taba kade wani almajiri da mota a kan titi, maimakon mutane su nemi ya bayar da kudin magani a kai almajirin kyamist tun da shi ba shi da mutuntaka domin ba ya ganin almajirin mutum ne kamarsa don ko taba shi bai yi ba, sai suka zo suna ba shi hakuri. Har da cewa: Ai da ma haka almajirai suke ba sa jin magana. Haka mutakabbirin ya hau mota ya wuce! Shi kuwa bawan Allah yana ta nishi har ya samu da kyar ya taka. Su kuwa mutanen ba mai ji a jikinsa cewa an ji wa wani mutum daga cikin mutane masu hakki kamar kowa ciwo! Wallahi da dabba ce aka kade da sun fi ba ta muhimmanci!. Daga cikin hakkin mutun a kan dan’uwansa mutum taya shi bakin ciki idan wani abu ya same shi musamman ma dan’uwa na jini ko na Addini da makwabci, kamar idan an yi masa mutuwa to ya kamata ne bisa koyarwa ta Manzo (S.A.W) a yi abinci kwana uku daga makwabta ana kai musu kamar yadda ya koya mana kyawawan dabi’u da fadinsa: “Ku yi wa iyalan Ja’afar abinci hakika wani al’amari da ya shagaltar da su ya same suâ€[34]. Amma abin sai ya zama bisa akasi, maimakon a kai gidan mutuwa, sai ya zama su ne kuma za a shagaltar da su da ciyar da masu taruwa. Idan muka waiwayi alakar mai kudi da yaronsa al’amarin ya kai ga ana iya samun yaron Alhaji da rashin lafiyarsa bai fi a kashe kudi kankani a kansa ba ya warke amma yana iya mutuwa alhali Alhajin da ya yi wa hidima a gida, da shago, da kanti, shekaru masu yawa yana gani sai dai ya mutu. Wani kuma yana aiki karkashin uban gidansa amma canja riga mai tsada yana iya tayar da mugunyar tsatsar nan ta hassada a zuciyar uban gidan, sai ya ce da shi: Ka tattara naka ka yi gaba kuma ka bar min shagona. Akwai wata kabila da galibinsu ba ma musulmi ba ne amma har bikin yaye yaron shagonsu suke da shi. Idan kuwa ka duba bangaren kere-kere to a nan sun yi nisa, sannan wasu abubuwan idan kana nemansu ranar lahadi to lallai ka wahala domin sun kulle shaguna. Don haka idan ana son mafita da ci gaba ya zama dole ne a siffantu da siffa ta gari a bar hassada da kyashi, a cire duk wata dauda daga zuciya. Idan wani ya ci gaba ta hanyarmu sai mu gode wa Allah, amma rashin kishin kai da son ci gaban juna, da rashin kyawawa dabi’un musulunci ya sanya ana danne hakkin juna, kuma mu sani cewa dukkan ayyukanmu suna da hisabi a Lahira. Hakkokin Mai Mulki Da Wanda Ake Mulka
Wannan yana iya bayyana ne ta hanyar sanin wanene shugaba da siffofinsa, domin idan mun san siffofin mai mulki to muna iya gane wannan alaka ta hakkokin mai mulki da wanda ake mulka: Daga cikin siffofin shugaba su ne; ya zama mai karfin tafiyar da mulki da Iliminsa da basirarsa, mai karfin zartarwa, kuma amintacce, wanda ba ya cin amanar al’ummar kasarsa. Mai neman maslaha ga al’ummarsa, mai daukarsu a matsayin ‘yanuwansa, maras tsanantawa a kan mutanensa. Kuma mai sakin fuska, mai hankali, da ilimi, da adalci, mai karbar shawara daga mutanensa wajan gudanar da al’amuranta, mai daidaitawa tsakanin mabiyansa ba tare da son kai ba ko fifita wasu kan wasu. Haka nan ya kasance mai kwarjini, mai kyawawan dabi’u da son gyara, mai hidima ga mutanensa, masanin siyasar Duniya da al’amarin tafiyar da al’umma, mai karbar nasiha daga talakawansa ko wakilansu, mai saukin hali. Ya kasance ba ya daukar fansa kan abokan hamayya, kuma mai kyauta ba marowaci ba, mai kaifin basira da yakan iya mayar da makiyi masoyi saboda kyawawan halaye da basirarsa, mai tausasawa ba mai tsanantawa ba. Duba wasikar da Imam Ali (A.S) ya rubuta wa Malik Ashtar yana cewa da shi: “Ka nisanci fushin al’ummarka domin fushinsu yana tare da fushin Allahâ€[35]. Mu sani cewa idan shugaba zai kalli kansa ne to lallai zai fada cikin fushin al’umma domin su ba su da abin da yake da shi, wasu shugabannin sukan kara kudin kaya ba ruwansu da talaka, sai ka ga al’ummar ta koma tana kinsa ba ta ganinsa daya daga cikinta, da zai wuce tana iya jifansa.
|