Hakkoki A Musulunci



Na biyu, ana bukatar ma’aunin waye maganarsa ta fi zama hujja don ka yi aiki da ita, wannan duk ya shafi makomarka ne.

Haka aka haramta wa al’ummarmu sanin Akidu da ilimomi har ka san menene gasakiya ka bi, menene a ganinka ba daidai ba ne ka bari. Duba ka ga ni mana Shehu Dan Fodia (R.A) yana ganin daga cikin bala’in da ya game kasashenmu na Hausa shi ne koyi a Usuluddin amma har zuwa yanzu abin da Shehu ya so a kawar na koyi a Usuluddin ya ci gaba. Koda yake wasu malamai sun tafi a kan cewa; wanda ya fadaka, ya yarda har a zuciyarsa, ya yi imani da samuwar Allah da kadaita shi a bisa sahihiyar Akidar musulunci, duk da tun yana yaro ya yi koyi da malamai ne ko iyaye, amma irin wannan imanin yana isarwa gare shi.

Hakkin Da Yake Kan Annabawan Allah

Annabawa (A.S) sun zo ne domin motsa hankali[16] ya yi tunani ya yi imani a Akidar samuwar Allah da kadaita shi a ibada da zatinsa da siffofinsa da ayyukansa, da kuma yarda da annabawan da ya aiko da riko da sakonnin da suka zo da su. Annabawa ba su ce a bi su ido rufe ba dalili ba, wannan al’amari ne ya sanya Allah yake ba su mu’ujiza da take dalili ce na hankali a kan cewa sakon da suke dauke da shi daga gareshi ne, wannan kuwa zai samar da nutsuwa a zukata har su karbi sakonsa.

Amma hukuncin furu’a (hukunce-hukunce) su an sanya su bisa biyayya da maslaha ne wacce ba kasafai aka santa ba sai dai a bi umarnin Allah a ciki, don haka ne Allah yake sanya wa kowane Annabi (A.S) wasiyyi da zai yi wa mutane bayanin abin da sakon ya kunsa bayan wafatinsa, kamar yadda annabin rahama (S.A.W) ya yi wasiyya ga wannan al’umma da imam Ali (A.S) da goma sha daya daga ‘ya’yansa a bayansa.

Matsalolin da wasiyyan Annabi suka fuskanta na kawar da su daga fagen jagorancin al’umma a hukumanci da kisa sun sanya Allah (S.W.T) ya boye na karshensu imam Mahadi (A.S) domin kada a kashe shi domin ya zo a karshen duniya ya cika ta da adalci bayan an cika ta da zalunci. Shi kuma imam Mahadi (A.S) kafin ya boyu ya yi wasiyya da riko da malamai na gari. Saboda haka duk wanda ya kai matakin Ijtihadi wato ya daukaka kan sauran mutanen duniya gaba daya a ilimi, da takawa, da adalci, da kamala, da tsentseni kuma ya kasance dan halal ne, to ya zama dole ne a bi shi[17].

Hakkin Imami (Shugaban Zamani) A Kannu

Sanin Imamin lokacinmu yana daga cikin hakkokin Allah a kanmu, domin duk wanda ya mutu bai san Imamin zamaninsa ba ya yi mutuwar Jahiliyya[18], haka nan ya zo a Kur’ani mai girma cewa a Ranar Lahira kowace al’umma za a kira ta tare da imaminta ne[19]. Wadannan imamai Allah bai bar mu mun zabe su da kanmu ba sai da ya shelanta su ta hannun Manzonsa (S.A.W)[20] wanda ya sanar da mu cewa su goma sha biyu ne: Na farkonsu Ali (A.S) na karshensu Mahadi (A.S) wanda yake shi ne imamin wannan zamanin.

Sanin Imam ba wai kawai sanin sunansa ba ne, saninsa ya hada da binsa kuma da koyi da abin da ya bari na wasiyyarsa kuma da bin koyarwarsa da malaman da suke shiryarwa zuwa ga abin da ya bari da kin makiyansa[21]. Al’amarin ba wasa ba ne kamar yadda wasu suke dauka domin ko Salla da Azumi da duk wata ibada idan babu mika wuya ga Imami Allah ba ya karba. Manzon tsira (S.A.W) ya ce: “Wanda ya mutu bai san Imaminsa ba ya yi mutuwar Jahiliyya”[22]. Domin zai tashi a Ranar Lahira kamar wanda ya yi zamani kafin a aiko Annabi ba shi da komai da Allah (S.W.T) ya karba daga gare shi.

Hakkokin Littafin Allah A Kanmu

Karanta littafin Allah da saninsa suna daga cikin hakkokinsa a kanmu, amma sanin littafin ba yana nufin mu san sunansa ba kawai domin hakan ko kadan ba shi da wata ma’ana, amma abin nufi shi ne ya zama mun siffantu da Kur’anin a aikace. Idan ba haka ba a ranar lahira akwai kara da zai shigar a kotun Allah[23] wacce ba a zalunci a nan kuma ba a iya boye gaskiya. Kuma dole a bi shi kamar yadda Manzo da wasiyyansa goma sha biyu daga Alayensa suka fassara domin su ne ya ce: “Idan an yi riko da su ba za a taba bata ba har abada”. kuma “Da Su da Littafin Allah ba sa rabuwa har sai sun riske shi a tafki”[24].

Haka nan al’amarin yake a matsayin al’umma, dole ne Littafin Allah ya yi iko da rayuwarmu a matsayin al’umma, in ba haka ba, ba mu sauke nauyin da yake kanmu ba. Kuma dole ne mu siffantu da shi, in ba haka ba, yana da hakkin karar cewa musulmi sun bijire masa.

Hakkokin Addini A Kanmu

Addinin Musulunci yana da hakki na kare shi a kan kowane musulmi da bakinsa da basirar da Allah ya ba shi, da wajabcin saninsa da taimakawa wajan yada shi a aikace[25] da baki da kyawawan dabi’u, da kokarin hada kan mabiyansa, da raddi cikin hikima ga masu gaba da shi, da girmama fahimtar ma’abotansa don ba ka sani ba ta yiwu shi mai waccan fahimtar da ta saba da taka shi ne yake a kan daidai.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 next