Hakkoki A MusulunciA musulunci fagen siyasa fage ne mai fadi da ya hada da horo da kyakkyawan aiki da hani daga mummunan aiki wadanda suka kunshi kira zuwa tsayar da tsarin musulunci, da kalubalantar azzaluman shugabanni, da karkatattun tsare-tsare na zalunci, kamar yadda suka kunshi shiga cikin gudanar da shugabanci, da tsarin siyasar al’umma, wayar da kan mutane a fagen siyasa, shawara da mubaya’a kamar zaben shugaba da wakilan al’umma, shiga cikin wakilcin al’umma a majalisu da muke kira da ‘majalisun wakilai, wadanda suke aikin horo da kyakkyawa da hani daga mummuna ta fuskar siyasa. Wannan yana nufin wajibcin shigar mace yadda ya kamata cikin jama’a da ayyukan siyasa, da kungiyoyi, da jam’iyyu, da cibiyoyin tunani, da kawo gyara, matukar aiwatar da wajibai kamar yadda ake bukata ya ta’azzara. Daga wadannan asasai na Kur’ani zamu fahimci cewa rayuwar siyasa a musulunci a bude take ga mace kamar yadda take bude ga namiji a dukkan matsayinsu na wajibi Aini da Kifa’i, ko halaccin shiga cikin rayuwar siyasa da dukkanin al’amura na zamantakewar al’umma. Godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai Masdarorin Madogarar Wannan Littafin:
Kur’ani mai girma Sharhu risalatil hukuk Tauhid, saduk Al’intisar, amuli Ma’asatuz Zahara, murtadha amuli Alwilayatut takwiniyya alhakkud dabi’I lilma’asum, jalal sager
|