Hakkoki A Musulunci



Ya ce: Maza ka tafi zuwa gare shi ka yanke dawafin.

Na ce: Koda ya kasance dawafin wajibi?

Ya ce: Na’am.       Abana ya ce: Sai na tafi, bayan nan -wani lokaci- sai na shiga wajansa (A.S) na tambaye shi game da hakkin mumini. Sai ya ce: Bari kada ka kawo wannan! Ban gushe ba ina sake tambaya har sai da ya ce: Ya Abana ka raba masa rabin dukiyarka, sannan sai ya kalle ni ya ga abin da ya shige ni, sai ya ce: Ya Abana ashe ba ka san Allah ya riga ya ambaci masu fifita wasu a kan kansu ba?

Na ce: Haka ne!

Ya ce: “Idan ka ba shi rabin dukiyarka ba ka fifita shi ba, kana fifita shi ne kawai idan ka ba shi daya rabin!

Na ce[56]: hakika a yanayinmu mai ban kunya bai dace ba mu kira kanmu muminai na hakika. Mu muna wani waje ne, koyarwar Imamanmu (A.S) tana wani wajen. Kuma abin da ya Shigi zuciyar Abana zai Shigi zuciyar duk mai karanta wannan hadisin, sai dai ya juya fuskarsa kawai yana mai mantar da kansa shi kamar wani ake wa magana ba shi ba, kuma ba ya yi wa kansa hisabi irin na mutumin da yake abin tambaya.

Hakkokin Kawukanmu A Kanmu

Kawukanmu da gabobinmu suna da nasu hakki a kanmu[57] saboda haka haramun ne mu cutar da kanmu cutarwa ta Lahira kamar mu yi sabo da su wanda zai jawo musu azaba, haka ma cutarwa ta Duniya kamar kin cin abinci da shan ruwa, da kin shiga inuwa, da shan guba. Don haka ne ma wasu malamai suka haramta shan taba don tana cutarwa. Kodayake malamanmu suna cewa: Ba ta zama haramun da farko amma in ta kai matsayin in mutum ya sha tana cutar da shi to a nan ta zama masa haramun[58].

Mafi munin zaluntar kai shi ne hana kai sanin Allah da manzanninsa da Ilimin aikace-aikace da suka shafi Sanin Duniya da Lahira na dan Adam, idan mutum bai san Allah ba sai ya kamanta shi da halittu sai ya bauta wa Allah (S.W.T) yana mai shirka da shi.

Masu hikima suna cewa: Sanin kawukanmu ya dogara kan amsar wadannan tambayoyi ne kamar haka: Ni wanene? Daga ina nake? A ina nake yanzu? Kuma Ina za ni?.

Rayinmu tana bukatar irin nata abincin da abin shan kamar yadda jiki yake bukata, mafi dadi a ciki shi ne sanin Allah da ganawa da shi ta hanyar addu’o’i da sauran ibadoji, amma babban asasi shi ne saninsa da farko, domin in ba sanisa yaya za a gana da shi?[59] Rashin sani ko wane iri ne yana daidai da sanya rai a kurkuku ne.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 next