Auren Mace Fiye Da DayaBayan an tashi sai ta yi ta godiya ta kuma ba ni labarin takaici da ke zuciyarta na ganin sauran mata da mazajensu amma al’ada ta tsananta a kan rashin yarda da auren mace sama da daya, ga shi kuma an tsananta mata a kan ba za a yarda ta zama ta biyu ba a gidan mijinta, hada da maganar cewa ita bazawara ce. Ta ce da ni: Maganar ta karfafeta ta auri mai auren, ai ita za ta yi wa kanta zaman. Amma duk da wannan yardar da ta yi har yanzu ba ta samu auren ba. Haka ma ya taba faruwa a Jamus mata suka nemi auren mace fiye da daya ya zama doka don ga sunan da yawa ba aure, amma Gwamnatin ta matsa wa coci kar ta yarda da haka, aka yarda da zina da fasadi ya yi yawa mai makon auren mace fiye da daya[4]. Ma’anar Auren Mace Fiye Da Daya
Da aka ce ya halatta kowa ya yi auren mace fiye da daya ai ba ana nufin kowa ya yi ba ne, abin da ake nufi shi ne ya halatta idan zai iya adalci kuma sharadi ne mace ta yarda zata aure shi, wannan sharadi hakki ne na mace da zata yi aure koda da wanda ba shi da mata ne. Don haka da zata ce ba ta yarda ta auri mai mata ba, da ba ta yi laifi ba a mahangar musulunci, haka nan da namiji ya ki auren mace sama da daya a shari’ar musulunci bai yi laifi ba. Dokar an sanya ta ne don wanda suka ga dama kuma zasu iya, asali ma da wani ya ce ba zai yi aure ba bai yi laifi a shar’ance ba matukar zai iya kare kansa da kamewa daga fasadi. Haka nan Musulunci ya sanya sharadin adalci ga namijin da zai auri mace sama da daya kuma ya sanya yardar wacce za a aura. Musulunci ya gindaya sharadin adalci tsakanin mata a zaman tare, da kwanan daki, da ciyarwa, ba kowa zai iya ciyar da ko da biyu ba sai mai yalwa, sannan kuma akwai hanya ta Addini ta shari’a da mace za ta iya sanyawa na kada a yi mata kishiya, kamar idan ba ta so kuma suka yi sharadi yayin aure kan cewa ba zai mata kishiya ba to dole ne ya kiyaye sharadin. A Amsar Suka Na Uku
Abin da kuka fada a nan ya nuna jahilcinku da shari’a da kuma dan Adam, domin shari’a ba tana kwadaitarwa ba ne ga sha’awa, abin da take so shi ne sanya dokoki domin kada a kai ga fasadi, shi ya sa aka bayar da hanyar warwara ga Dan Adam. Abin da ya tabbata shi ne; galibi namiji ya fi mace saurin sha’awa, saudayawa mace idan ta rayu a tarbiyya zaka ga wannan tarbiyyar da kunya sukan taimaka mata nisantar namiji sosai, amma namiji sai dai ya tarbiyyatar da kansa domin sha’awarsa tana kusa, shi ya sa ya fi mace sha’awa da yawa. Haka ma ba kasafai yake mallakar kansa ba, namiji yana da sha’awar mata biyu ko uku ne, shi ya sa daga hikimar Allah ya ba shi damar auren mace fiye da daya don kada ya yi tawaye ga hankalinsa ya bi sha’awarsa, sai a ka ba shi dama da ya tara mata a gidansa kar ya kai farmaki da sha’awarsa wajajen fasadi.
|