Auren Mace Fiye Da Daya Misali Na Biyu: Da musulmi zai saba wa maslahar musulunci da ba laifin addini ba ne don an gina shi a kan maslaha ne, shi ya sa ma idan dokarsa ta saba da masalaharsa to a ka’ida sai a ajiye dokar gefe. Muna iya ganin misali a hukuncin musulunci kan munafukai amma Manzo (S.A.W) ya bar su domin maslahar addini domin kada a ce Muhammad yana kashe sahabbansa[16]. A tarihin Musulunci akwai cikin halifofi wanda ya dage sai ya yi kisasi tsakanin wani musulmi da wani malamin kirista da ya musulunta saboda ya mare shi, maimakon ya sa musulmin ya yafe sai ya gwammace wancan kiristan ya koma kirista shi da mabiyansa gaba daya, musulunci ya yi hasararsu, suka koma kasar Rum suka ci gaba da gaba da Musulunci[17]. Wani ya ce da ni wannnan ya nuna ke nan da ma musulunci bai shige shi ba. Sai na ce: Ai shi in bai shige shi ba to ‘ya’yansa fa? ba ka ji kissar Bayahuden da yake cewa ‘ya’yansa “Tankiye mi kardam[18]†a lokacin da zai mutu ba. Wannan kissar wani bayahude ne da yake bayyanar da musulunci amma yana boye yahudanci, da zai mutu sai ya ce da ‘ya’yansa: Kada su binne shi a makabartar musulmi, sai suka yi mamaki yaya haka, sai ya ce da su: Tankiye mikardam. Wato yana yi wa musulmi boyon hakikanin Addininsa na Yahudanci ne don ya rayu cikin soyayyar kowa a matsayin dan’uwansu na Addini. Idan mun duba zamu ga ‘ya’yansa sun zama muminai masu imani na gaskiya. Yarda da komawar wancan malamin kirista ba ya nuna zurfin adalcin halifa, abu ne wanda ya saba wa maslahar musulunci, idan dai Manzo (S.A.W) ya bar kisa don kare musulunci don me mari ba zai baru ba?. Karanta Suratut Tauba da Munafikun ka ga halinsu, amma aka kyale su don kare maslahar musulunci, haka nan abin yake a musulunci. Da Manzo (S.A.W) ya kashe su da fitina babba ta faru a musulunci domin ba za a samu masu shigarsa ba don ana kashe ma’abotansa. Fa’ida ta biyu kuma shi ne ‘ya’yansu da suka ta so su sun taso da ikhlasi da imani na gari, wannan haka yake duk wani Addini da wani ya karba ba da gaske ba to su ‘ya’yansa zasu ta so da shi cikin ikhlasi da yarda da shi. Sakamakon haka a nan halifan musulmi ne ya yi kuskure da ya saba wa sunnar annabi, kuma wannan kuskuren ba shi ne musulunci ba saboda haka ba mai iya jingina wannan kuskure ga musulunci. Misali Na Uku: Idan wani ya yi saki yana musulmi ba shaidu biyu adalai ba ta saku ba kuma a wajan Allah matarsa ce, wannan ita ce mahangar mazhabin Ahlul Bait (A.S). Da wani zai aure ta da ya auri matar wani ne domin wannan rashin tsari musulunci bai zo da shi ba. Allah (S.W.T) yana cewa: “Ku sanya shedu biyu adalai daga cikinkuâ€[19]. To idan musulmi bai kiyaye wannan ba, ko bai bari ta yi tsarki ba ya sake ta, sai saki ya yi yawa barkatai ba tsari[20], ba yadda za a jingina wannan da musulunci, idan ya zama musulmi sun saba, sai yawan saki ya faru wannan ba matsalar musulunci ba ce ta su musulmi ce. Sannan don me ya sa ba kwa ganin yawan sakin da yake kasashenku, da kashe-kashe, da fyade, don me ya sa ba kwa jingina shi ga Kiristanci da sauran addinan wadannan yankuna. Misali Na Hudu: Da wani mutum mai auren da ya saki matarsa ya yi zina sai aka kashe shi da jifa don ya taba yin aure, da ya rataya a kan musulmi, don an kashe shi maimakon bulala, saboda Allah (S.W.T) bai ce a kashe shi ba, Mutumin da Allah ya yi umarni a jefe in ya yi zina shi ne muhsini, wane ne muhsini? shi ne wanda Ahlul Bait (A.S) suka ce: “Yana da farji da yake zo masa safiya da yammaâ€[21].
|