Auren Mace Fiye Da DayaHaka nan namiji kodayaushe a sake yake; hutawa, da koshi, da nishadi, suna iya samar da bayyanar dabi’ar jikinsa, don haka dole ne a samu doka da tsari a rayuwarsa, don haka wadanda suke sukan tsarin musulunci a fili yake cewa su suka fi cancantar irin wannan suka da zargi. Kuma musulunci bai yarda da yakar dabi’a ba don ba kowa ke iyawa ba kuma wannan ya saba wa hankali, shi ya sa ya bayar da dama ga wanda zai iya adalci ya auri fiye da daya, kuma idan yanayi ne da zai kai ga fasadi kuma ba ka iya yin haka to ya ba ka dama ka yi auren mutu’a. Bai ba ka da ma ba ka yi zina ta kowane hali, haka nan bai ce ka yaki dabi’a ba don ba ma zaka iya ba. Amma masu sukan ba su tanadi irin wadannan dokoki ba masu hikima da zasu kare al’umma daga fadawa fasadi, don haka sai namiji ya jefa ruwansa duk inda ya ga dama ya kuma wuce ba ya kunyar Allah ba ya kunyar mutane. Shi ya sa mista John Dibon a Risalarsa yake cewa: “Ba abin da ya jawo mummunan yaduwar fasadi a duniya fiye da hanin da coci ta yi wa auren mace fiye da dayaâ€. Amsar Suka Na Hudu
Ba kamar yadda ku masu suka kuka dauka ba ne domin musulunci bai takaita wannan rayuwa ta auratayya a bisa dabi’ar so kawai ba, aure wani abu ne wanda aka gina shi bisa hankali, don haka ne shari’a ta gina aure bisa asasin hankli da kuma kauna, so dabi’a ce kuma abu mai kyau amma ba shi ne ma’auni ba. Sannan babu wani Addini da ya girmama mace irin musulunci a duniya gaba daya, ku sani musulunci ya kafu bisa doka ta hankali ne don haka ne ya kafa wadannan dokoki don tsara rayuwar namiji da mace ba don namiji ya fi mace ba. A musulunci ba wanda yafi wani tsakanin namiji da mace sai da tsoron Allah. Saboda haka su dokokin an gina su ne bisa masalaha ta zamantakewar dan Adam ba don wani jinsi ya fi dayan ba. Da wannan ya kasance domin fifikon jinsi a kan wani jinsin da babu wani ma’auni da zamu iya auna hakan da shi, domin akwai hukunce-hukunce da ba sa hawa kan mace, babban misali a nan shi ne wajabcin yaki, amma ba mu taba ganin wani ya ce musulunci ya zalunci namiji ba. A misali: da mace zata iya auren maza da yawa da an rasa nasabar mutane, da kuma an rushe dangantaka ta mutane da sun koma kamar dabbobi kai mafi muni daga dabbobi don ba mai ganin wani nasa ne, ba mai karbar maganar wani da kima. Da wanda ya rike shugabanci ba ya jin shi dan al’ummar ne da al’umma ta fuskanci bala’oi masu yawa. Yaba Wa Musulunci Da Dalilan Sukan
Masana da dama ne a yammacin duniya suka yaba wa tsarin musulunci da shari’arsa, amma masu sukan sun dogara da abin da yake faruwa ne a gidajen musulumi wanda wannan kuskure ne babba domin ba a yi wa addinin mutane hukunci da al’adunsu. Sun duba sun ga wasu gidaje na musulmi ne da zaka ga namiji da mata masu fitina da rayuwa maras dadi, da hassada tsakaninsu, maimakon so ya cika gida sai so ya koma gaba, tausasawa ta zama tsanantawa, ba tausayi, ba rahama, ba so, ba zaman lafiya tsakanin miji da matan gida. Maimakon ya zama hutuwa sai ya yi zafi ya zama gidan azaba, da gaba, da bakin ciki, da wahala. Ga uba da ‘ya’ya duk rayuwa ta gurbace, dadinta ya tafi, wani lokaci ana ma iya kashe juna, al’amarin har ma tsakanin ‘ya’yan waccan da na waccan, uba ya tsufa nan da nan ana ma iya kai wa ga kashe shi. Suka ce: Sai dabi’un al’umma su lalace ta haka, kashe-kashe, da sace-sace, da fashi, da alfahasha, da saki, da aurace-aurace su yi yawa. Abin da kan iya sanyawa ba abin da maza suke yi sai su dandani wannan su koma kan waccan, suka ce; ba komai a cikin irin wannan rayuwa sai kawo tabewar mata da adadinsu ya kai yawan rabin wannan al’umma. Tambaya a nan ita ce: Wane waje ne a duniyar nan ya fi wajanku lalacewar al’adu da dabi’a ta yadda mace ta zama kowa ya ga dama sai ya dauka ya cimma burinsa da ita?. Duba ku ga kanku da kanku da furucin da kuka yi da kanku kamar yadda wani yake shaida mini cewa: Ai mu a yamma kowa yana jin yana rayuwa kamar shi kadai ne, abin da ya jawo yanzu musammam wasu matan sun fi son su auri bakin haure musamman daga Arewacin Afrika da sauran yankun kasashen musulmi da suke hijira zuwa kasashensu. Yaushe Mai Mata Daya Ya Tsira, Kuma Lalacewar Tarbiyya A Ina Tafi Yawa?
Sannan kuma duk abin da kuka fada kamar yadda yake faruwa ga mai mata da yawa yana faruwa ga mai mata daya. Duba ku gani kasashenku da suka fi ko’ina saki a duniya amma wannan ba don suna auren fiye da mace daya ba ne, misalin Amurka da saki ya fi ko’ina yawa a duniya, a cikin kasashen musulmi kusan Farisa da Turkiyya suna sahun gaba, amma yawancin wadannan kasashe ba kasafai ake auren mace sama da daya ba. Duba jadawalin sakamakon saki a Duniya a 1998 kasa ta daya Amerika 4.3. Sannan Rasha 3.4. Sai Ingila da Austaraliya 2.9. Sannan Kanada 2.4. Sannan Jamus 2.3. Sannan faransa 2.0. Sai Japan 1.9. Sai masar 1.1. Sai Thailand da Spain 0.9. Sannan barazil 0.6. Sai Turkiyya da Italy 0.5. Sai Meksico 0.4. Sannan clombia 0.1. sannan sauran kasashe su biyo baya[14].
|