Auren Mace Fiye Da DayaSuka Na Farko Auren mace fiye da daya zuwa hudu yana karya zuciyar mata sai su daina aikin gida, su nemi daukar fansa ma, da kin kula da tarbiyyar yara, kai suna iya cewa su ma bari su nemi wasu maza sai su shiga ha’inci da zina, da fasikanci, da barnar dukiya, da sauransu. Suka Na Biyu Auren mata hudu ya sabawa dabi’a domin ita dabi’a ta tanadar wa kowane namiji mace daya ne shi ya sa yawansu yake kusan daidaita. Suka Na Uku Auren mace fiye da daya zai kwadaitar da maza bin shwa’awa da zari, da son zuciya. Suka Na Hudu Auren mace fiye da daya ya saba wa shi kansa musulunci domin an ce: Namiji yana da ninki daya ne kan mace a gado da shaida da sauransu, me ya sa a aure har hudu ba biyu ba?[2] Amsar Suka Na Farko
Ku sani cewa Musulunci yana gina al’umma a bisa asasin rayuwa na hankali ne ba na dabi’ar zuciya[3] ba, abin da ake bi a musulunci shi ne hankali ba son zuciya ba, kuma wannan ba yana nufin an mance da dabi’ar ba ce, ko kuma rushe baiwar da Allah ya yi. Tarbiyyar da mata suke tashi da ita a wadancan nahiyoyi na masu sukan ta saba da wacce musulunci ya yi wa musulmi shi ya sa suke kawo irin wannan suka. Domin a al’adunsu mace ba ta da tunanin cewa ba ita kadai ba ce zata iya zama mace a gidan mijinta. Haka nan a sake suke sai ka ga namiji yana bin mata yana bin sha’awarwsa ga muharrama, da budurwa, da bazawara, da mai aure, da maras aure. Kai! da wahala a kirga mutum dari a samu kashi biyar cikin dari da ba su yi haramtarciyyar mu’amala da mata ba a rayuwarsu, wannan kuwa ko namiji ko mace. Ba su tsaya nan ba har sai maza da maza, mata da mata, suka yi kawance da juna, daidai ne suke tsira, har al’amarin ya kai ga an taba samu a majalisar wata kasa ta turai ake neman mayar da luwadi bisa doka, yanzu ana maganar shin dan shekara sha shida zai iya rijista a kungiyar luwadi da madigo ko kuwa? Amma mata musamman budurwoyi da marasa aure al’amarin ya yi muni sosai.
|