Auren Mace Fiye Da DayaRaddin Sukan Auren Mace Fiye Da Daya
Hafiz Muhammad Sa’id
hfaza@yahoo.com
Kuma idan kuka ji tsoron ba zaku yi adalci ba a game da marayu, to sai ku auri abin da ya yi muku dadi daga mata, biyu-biyu, ko uku-uku da hudu-hudu, amma idan kuka ji tsroron ba zaku yi adalci ba, to (ku auri mace) daya ko abin da hannayenku suka mallaka…[1]. Gabatarwar Mawallafi
Muna godiya ga Allah da ya ba ni damar rubuta wannnan littafi da na rubuta mai suna “Raddin Sukan Auren Mace Fiye Da Daya†kuma mai muhimmanci matuka a wajena saboda abin da ya kunsa na kariya ga Manzo (S.A.W) da kuma Addinin Musulunci musamman abin da ya shafi Auratayya da kuma Raddi Mun yi amfani da misalai domin cimma abin da muke son isarwa na fahimtarsa don kawar da shubuha da soke-soke da ake jifan musulunci da su, kuma da saukaka karanta shi ta yadda kowa zai iya karantawa kuma ya fahimta. Mun sanya yawancin dalilai da muke kawo wa domin tabbatar da hujjarmu da misalai da yawa a littafin domin ya zama ya fi dadin karantawa ga masu karatu. Muna son tunatar da masu karatu cewa wannan littafin an rubuta shi domin kowane irin mutum ya karanta shi koda ba musulmi ba ne, don haka idan ya saba wa mazhabarka sai ka sani yana kariya ga musulunci ne ba tare da la’akari da mazhaba ba. Ina rokon Allah ya bayar da ladan rubuta wannan littafi ga Dan’uwana Ahmad Muhammad ya haskaka kabarinsa da shi. Hafiz Muhammad Sa’id hfazah@yahoo.com Rabi’ul Awwal 1424 Khurdad 1382 Mayu 2003 Soke-Soke A
|
1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 | next |