Tsarin Siyasa A MusulunciHaka nan sayyid Ra’is Zadeh yana cewa: “Ban taba ganin wani nau’in tsari da imam Khomain (K) yake kin sa ba irin tsarin gadon mulkiâ€. Ya ce: “A bisa wane dalili ne kawai don an haife ka a wani gida shi kenan sai ka zama jagoran al’umma koda kuwa ka fi kowa dolanciâ€. Idan muka ga Allah ya zabi wani to ba doming gado ba ne, sai dai domin ya fitar da zuriya mai tsarki daga gida mai tsarki kamar yadda ya yi wa alayen Ibrahim; kamar annabi Is’ma’iI da Is’hak (A.S), ko kuma alayen Imrana wanda su ma annabawa ne da wasiyyansu, ko kuma annabi Dawud da Sulaiman (A.S) ko kuma abin da ya yi wa alayen Muhammad (S.A.W) wanda ya hada tun daga dan’uwansa Ali (A.S), kuma ya sanya zuriyarsa tsarkaka sha daya daga gareshi da shi da ‘yarsa Fadima (A.S) tun daga Hasan (A.S) har zuwa Mahadi (A.S). Wannan kuwa ya yi kamar yadda mutum yake kera motoci sai ya yi wasu masu shakali mai kyau da jan hanakli wasu kuma sai ya yi su masu saukin kudi da karancin jan hankalin mutane da karancin inganci. To haka nan Allah mai hikima yake yin halittarsa da bambanci yadda ya so, don haka ne ma kamar yadda mai yin mota ya yi wata tana da karfi da gudun 280, wata kuma ya yi ta da rauni da gudun 120, sannan kuma ba ya ganin laifin mai 120 domin ta kasa gudun mai 280. To haka nan Allah mai hikima ya yi mutane; sai ya yi annabawa (A.S) da wasiyyansu ya yi su ma’asumai saboda ya ba su ilimin hakkun yakin da ainul yakin da ilmul yakin ta yadda suna iya ganin gaskiya kamar yadda take. Amma sai ya yi sauran mutane da yawanci sun rasa hatta da ilmul yakin balle su kai ga ainul yakin balle kuma karshe hakkul yakin. Don haka ne ma bai dora wa su sauran mutane nauyin da ya kai na wadancan masu daraja ba. Sannan kada mu manta cewa; duk da Allah madaukaki ya ba wa annabawa da wasiyyansu (A.S) ikon tafiyar da al’umma amma bai ba su ikon tilasta mutane su bi su ba, sai ya ba wa al’umma zabi idan sun zabe shi to ya kafa hukuma, amma idan ba su zabe shi ba ya ci gaba da shiryar da su daidai gwargwadon abin da zai iya yi kamar yadda dai muka riga muka yi bayanai a baya. Wannan kuwa a cikin maganganun imam Ali (A.S) musamman a Nahajul Balaga muna iya fahimtar hakan, hada da abin da ya zo na tarihi a cikin littafin Kur’ani mai girma da ruwayoyin manzon Allah (S.A.W). Al’amarin hukuncin bin Allah bisa tilas ko bisa zabi da biyayya zai wakana ne da bayyanar Imam Mahadi (A.S)! Mene ne sharuddanjagora da ayyukansa?
Sharuddan jagora a takaice kamar yadda na yi wani bincike a kai sun hada da: Mai yawan Ilimi kuma masani kan abubuwan da suke gudana; mai cikakken hankali; mai kyawun jagoranci; mai adalci; mai takawa; mai gaskiya; mai madaidaiciyar dabi’a; mai karfi; mai dacewa; mai lafiya; mai yin shawara; masanin zamaninsa da addininsa; masanin al’amuran tafiyar da al’umma; wasu sun kawo ya kasance namiji; mai ba wa kowa ‘yanci da daidaito; mai daidaita kowa a gaban doka; mai duba bukatun mutane; mai biyan bukatun talakawa; mai daidaito a bayarwa; mai kyakkyawar mu’amala; mai tarbiyyantar da al’umma; ya kasance baligi; mai gabobin masu lafiya; kada ya kasance dan zina; ya kasnce da ba bawa ba; ya kasance ba ta karfi ya hau mulki ba; mai kwarjinin da idan ya yi umarni za a bi; mai tausayi; mai kariya ga kasa da al’umma; mai kusanto da talakawa kusa da shi; mai yafewa tare da yana da iko; mai kyautata wa kowa; mai game kowa a cikin al’amarin kasa da hakkoki; kada ya kebanci na kusa da shi da arzikin kasa; mai farkawa kan komai; mai tsananin kiyayya da zalunci; mai kankanda kai; mai kyakkyawar zuciya; kada ya kasance fajiri ko faskiki; mai kula da muhimmantar da al’amuran al’umma; mai zabar maslahar al’umma kan maslaharsa; mai nasiha ga mutane; mai yalwata musu rayuwarsu; mai hakuri matuka da juriya; mai iya bayani; mai ilmantarwa; mai koyar da tarbiyya; amintacce ba mai cin amana ba; mai ikhlasi da sadaukarwa; mai karfin imani da kyawawan halaye; mai sauraron kukan jama’a da kokarin warware matsalarsu da gaggawa; mai tsananin tsoron Allah; mai biyayya ga dokokin Allah; mai ayyuka nagari; mai karfin zartar da umarnin Allah sabanin son ransa; mai tsayar da haddi koda kuwa kan nakusa ne; maras tasirantuwa da sanayya; mai tsananin tausayi da yin afuwa ga mai laifin da shari’a ta ba shi damar yin afuwa; mai kauna da rige zuwa ga tafarkin Allah; mai yalwar kirji da tunani; mai kaifin kwakwalwa; mai karbar nasiha a boye da sarari; wanda ba ya daukar fansa kan abokan hamayya; mai bin hanyar daidai wajen ayyukansa babu yaudara; mai amsawa bukatun al’umma; mai amsa kiran al’umma; maras kwadayin duniya da kyale-kyalinta; mara zari da handuma; maras cin amanar al’umma; mai kame kai; mai kunya; mai karimci da kyauta; mai nuna daidaito ga al’umma; maras tsoro; maras rauni; mai hikima; maras dimaucewa; maras kwadayin shugabanci; maras raunin siyasa; mai kyakkyawan shugabanci; mai iya tafiyar da al’amuran al’umma da kyau; mai sanya tausasawa a ayyukansa; mai duba farko da tsakiya da karshen abu kafin ya aiwatar; mai kula da yardar al’ummarsa; mai tsantseni; mai tarbiyyar kansa da yi wa kansa hisabin ayyukansa a kullum; mai karbar shawara; . Ayyukan jagora:
Kare addini da isar da shi; gyara al’amarin mutane; raya sunna; tsayar da haddodi; kokarin ayyukan alheri; yin wa’azi da shiryarwa; yada adalci ga al’umma; yakar makiya da kare al’umma; karbar hakkokin Allah; ayyana shugabannin ayyuka ko cire su; kiyaye hakkokin al’umma; raba arzikin kasa da hidima ga mutane; yin shawara da mutane; nisantar fushi; jawo yardar mutane; raya addini; kula da hakkokin raunana da marasa rinjaye; bayar da ‘yancin bayani da suka; alaka da mutane; kula da ayyukan tausaya da jin kan raunana wato miskinai da talakawa; kiyaye tsaron al’umma; kiyaye dukiyar al’umma; kiyaye kasuwanci da hana boye kaya; raya kasa da gine-gine domin samar da kowa gidan zama; yakar talauci; samar da aminci; yada kyawawan halaye; sanya shugabannin ayyuka nagari salihai; jarrabawa ga wakilai kafin ba su ayyuka muhimmai kamar jarraba amanarsu da kunyarsu da kamewarsu; samun mutanen da suka fito daga gidaje nagari domin ba su ayyuka muhimmai kamar wakilci, kula da addinin wanda zai ba shugabanci; sanya ido kan ma’aikatansa; yi misi hisabi mai tsanani; karfafa su da kuma yi musu gargadi; hukunta su idan sun saba; Saboda kasancewar muna son daukar hutu in Allah ya so wannan bahasin da yake yana da tsayi zamu cigaba da shi nan da wata uku; Sannan kuma in Allah ya so zamu kawo bayanai game da Imam mahadi (A.S), kodayake kusan shekara guda kenan (idan ban manta ba) rajab ko sha’aban ko Ramadan na taba ganin wani ya buga wasu bayanai da muka sanya a wani sayet da kuma wanda muka buga a game da Imam mahadi (A.S) a wata jarida ta musulunci ta hausa amma sai ya sanya sunansa kawai, ina ganin a rika kiyaye amanar ilimi a rika fadin inda aka nakalto kasidoji! Hafiz Muhammad Sa'id Kano, Cibiyar Al'adun Musulunci, August 2008
|