Tsarin Siyasa A Musulunci1- A amsa ta farko muna iya ganin a fili yake daga abin da ya zo a koyarwar musulunci shi ne; bai halatta ba mutane su zauna babu jagora da shugabanci, don haka wajibi ne su samu shugaba ta fuskancin wajebcin kiyaye tsarin al’umma. Sannan kuma wannan yana daga babin ture fasadi babba da fasadi karami ne, don haka ne ma imam Ali (A.S) yake cewa; dole ne a samu shugaba ga mutane nagari ne ko fajiri. Kuma mun riga mun yi nuni da ma’anar fajiri a nan da cewa; yana nufin wanda ba bisa dokar asali ta Allah (S.W.T) yake jagorantar mutane ba, wato jagorancinsa babu lasisi daga Allah madaukaki mai kowa mai duka. Don haka ne ya wajaba a girmama wannan shugaban koda kuwa ba bisa ka’ida yake ba, sai dai idan ya yi umarni da saba wa Allah madaukaki, to a nan ba za a bi shi ba. Kuma idan zabi ya kasance tsakanin samun wannan jagora da rashin jagora dole ne mutane su yi riko da jagorancinsa su kuma yi kokarin samar da wannan tsarin. Kuma kokarin kawar da wannan tsarin ta yadda zai kai ga mutane ga rasa wannan tsarin saba wa ne. Amma shugabanci da muke gani na kungiyoyi ba ya cikin abin da ake magana a kansa, domin shi ya doru ne bisa “…Ku yi taimakekeniya a kan kyakkyawa da takawa, kada ku yi taimakekeniya a kan sabo da ketare iyake…â€. Don haka duk sa’adda wasu mutane suka hadu suna iya kafa kungiya ta ayyukan alheri ta yadda zasu taimaka wa al’ummarsu ta hanyoyi da dama, ilmantarwa, kula da lafiya, kula da tsaron yankunansu, gyaran hanya, da hanyoyin ruwa, da titian, da kafa cibiyar motsa jiki da wasanni da makamantansu. A nan mutane suna iya kafa dokokin da suke na maslahar zamantakewarsu da kuma tafiyar da kungiyarsu bisa kyakkyawa matukar dokokin ba su saba wa kykkyawar al’ada ko addini ba. Irin wannan shugabanci abu ne da mutane mahankalta suka hadu a kan samar da irinsa kuma shari’a ta zartar da shi matukar bai kai ga keta dokokinta ba. 2- Kafin mu bayar da amsa ta biyu muna iya cewa; akwai nau’o’in shugabanci a rayuwar ‘yan’adam kamar haka: a. Na addini; kuma ya hada da: 1) wanda Allah ya yarda da shi kamar na annabawa (A.S) da wasiyyansu (A.S) da kuma wadanda wasiyyansu suka ba su lasisin jagorancin al’umma ta hanyar ayyana su kai tsaye ko kuma ba kai tsaye ba, kamar su fadi siffofin mutanen da suke iya jagorantar mutane kamar yadda wannan yake kunshe cikin littattafan addinai. 2) Da kuma wadanda ba su cancanta ba bisa dokar addini sai dai sun zo da sunan addini ne suka kwace mulki ta karfin tsiya. Ko kuma sun samu karbar jagorancin al’umma amma bisa gurguwar fahimtar addini wacce ba sahihiya ba. b. Na zabin al’umma: da ya hada da tsarin zabin gwamnati ta hannun al’umma kamar Demokradiyya, ko kuma tsrin jamhuriyya, da tsarin taho mu kafa gwamnati daya daga bangarorin wasu kasashe ko kuma daga kasashe daban-daban da makamantansu. c. Na kungiya kamar yadda kwaminisanci yake danne sauran al’umma ya sanya iko a hannun ‘ya’yansa kawai da karfin tsiya. d. Na wasu jama’a takaitattu saboda kawai suna da karfi ko ikon yin hakan kamar yadda sojoji sukan yi a kasashen duniya. e. Na gado kamar sarakuna da ake da su a kasashen duniya, kuma tsarin ne da babu wani ma’aunin kasancewar jagora shugaba sai domin kawai an haife shi daga wani gida sai ya gaji babansa. Kuma shi ma ya kasu gida biyu: imma dai mai sarki kawai, imma kuma mai sarki amma da majalisa. To dukkan wadannan tsarurrukan duka ba su inganta ba sai dai na farko shi ma wanda Allah ya ayyana da kansa, don haka duk sauran tsarurruka a mahangar addini ba su da kyau, muna ganin yadda sheikh Usman dan Fodio ya kyamaci mulkin sarauntar gado kuma ya kira shi da bidi’a don haka masu sukan sa ina ganin ba su yi mishi adalci ba domin an mayar da ita gado ne bayan mutuwarsa, Idan mun duba a cikin littafin Shehu Usman dan Fodio na “Najmul ikhwan Yahataduna bi iznil-Lahi Fi umurizZaman†zamu ga yadda yake kyamatar wannan tsarin har yana nuni da cewa; Farkon wanda ya bata al’amarin al’ummar musulmi shi ne Mugira bn Shu’uba yayin da ya ba wa Mu’awiya shawarar ya sanya dansa Yazid kan mullki. Kuma mun ga yadda dayawa daga sahabbai da ‘ya’yansu suka kyamaci abin da Mu’awiya ya yi na sanya Yazid dansa kan mulki har ta kai ga jayayya da barazana da Mu’awiya ya yi na fille kan su Abdullahi bn Umar da sauransu idan ba su yi wa dansa bai’a ba.
|