Tsarin Siyasa A Musulunci



Wani yana iya tambaya ya ce: To yaya zamu gane wadannan matakai sai in ce yana da wuya ka gane domin abu ne wanda yake bukatar shiriya daga Allah (S.W.T), kuma mutane sun ki yarda su karbi wannan shiriya don haka duk wani bala’in da suka fada su suka jiyo wa kansu, kuma duk da ba zamu iya ganewa ba saboda wahalar sanin wane yanayi ne, kuma wane mataki ne, kuma a wane lokaci ne, kuma waye zai yi, da sauran wahalhalu da suka dabaibaye wannan lamarin amma wasiyyin Annabi (A.S) na karshe ya zartar da matakan wadanda suka gaje shi suka san koyarwarsa suka dauki ilimi daga abin da ya bari suka kai matakin sani na koli duk da kuwa zai iya kasancewa cike da kurakurai, amma da yake bisa hasken doka ne don haka sai ya kasance kuskure ne wadannan manyan malamai zasu iya yi mai lasisi daga Allah, sabanin wani wanda ba a ba shi lasisi daga Allah ba ko Annabi (S.A.W) ko wasiyyin Annabi (A.S), kuma bai ma san koyarwarsu ba.

Wahalar wannan al’amarin ta kai ga cewa; tun da ake tashi domin gwagwarmayar yakar sarakuna masu mulki a cikin sama da shekaru dari biyu da hamsin na wasiyyan manzo (S.A.W) har zuwa karamar boyuwar wasiyyinsa na sha biyu kuma halifansa na karshe da ya yi albishir da shi, ba mu samu wata gwagwarmayar siyasa ta kifar da daula ba da ta samu goyon baya daga wasiyyan Annabi (S.A.W) (A.S) sai ta Mukhtar da ya dauki fansa ga makasan imam Husain (A.S) shi ma ba yarda ta karara ba ce, sai kuma gwagwarmayar Zaid bn Ali tare da karfafawar da suka yi cewa; ba za a taba samun nasara ba, al’amarin da ya kai ga kashe dukkan wadanda suka tashi suka yi wannan motsin.

Idan mun duba a fili yake cewa shugabannin addini na gaskiya da Allah da manzonsa suka ayyana sun riga sun bayar da matakan da ya dace a dauka na shiryar da al’umma zuwa ga tafarkinsu da tarbiyyarsu ga sanin Allah (S.W.T) da hakkokinsa da kuma hakkokin ‘yan’adam da kuma wadanda suka hau kansu, da kuma komawa zuwa ga malamai masu gadon tafarkinsu kawai banda sauran malaman da suke hana mutane saninsu kamar yadda suka kira su da sunan masu fashin imani wanda ya fi na rayuka da dukiyoyi muni. Kuma su ne zasu nuna yadda za a yi mu’amala da kowane mutum ne tun daga sarakuna da shugabanni da kowane jagoran wata al’umma ba tare da rikon su a matsayin su ne jagororinsu na shiriya ba, don haka rikon wani mutum daban jagora kuma shugaba mai shiryarwa ga tafarki sabaninsu to daidai yake da mutuwar jahiliyya!!!

2- Amma abin da ya samu duniya sakamakon kauce wa siyasar Allah (S.W.T) da jam’iyyarsa wannan wani abu ne da yake a fili, muna iya ganin yadda duniyar dan’adam ta bace kan al’amarin duniya da lahira ta fada cikin alakakai da surkukiya; amma al’amarin lahira a fili yake cewa mutane sun kasa sanin addinin gaskiya ko mazhabar gaskiya suna ta dimuwar da ta fi dimuwar shekaru arba’in ta Banu-Isra’ila muni, domin dimuwar yau ta rashin sanin gaskiya ce, wannan kuwa sakamakon ‘yan fashi da suka yi yawa a kan hanyar isa zuwa ga Allah madaukaki ne, sannan kuma dimuwa ce da ba wanda ya san sanda zata kawo karshe. Don haka kamar yadda suka dimauce kan al’amarin lahira ta yadda suke bin kowane irin kira doo. Haka nan ma suka dimauce kan lamarin duniyarsu ta yadda babu wani wanda ya isa ya fitar da duniya daga dimuwarta ta al’adu da zamantakewa da siyasa da tattalin arziki da tarbiyya da makamancinsu ta yadda zai fito da ma’anar adalci a kowane fage wanda yake nufin gaskiya a komai ba tare da tauyewa ba sai wanda yake ya san Allah (S.W.T) hakikanin sani wanda kuma babu wani wanda yake haka sai wanda Allah (S.W.T) ya zaba na annabi (S.A.W) ko kuma wasiyyinsa (A.S), amma su ma da sharadin al’umma ta yarda da jagorancinsu.

Amma abin da ya yake cikin tunanin wasu masu ganin cewa don me ya sa Annabi (S.A.W) ko kuma imami (A.S) bai dauki wasu matakai ba na shari’a? sai mu ce duk wannan yana komawa ne zuwa ga rashin yardar mutane; Misali me ya sa jagororin da manzon Allah (S.A.W) ya yi wasiyya da su ba su riki jagoranci ba? Sai mu ce: yana daga sharuddansu mutane su yarda da su sannan sai su riki jagorancin al’umma. Muna iya ganin yawancin annabawa (A.S) ba su riki jagorancin al’umma ba na tafiyar da mulkinsu saboda al’ummar ba ta yarda ba, don haka ne ma zabe yake da muhimmanci a wannan zamani namu, kuma shari’a ta ki yarda da wani ya jagoranci mutane koda kuwa annabi (A.S) matukar mutanen ba sa so.

Manzon Allah (S.A.W) yana cewa: Allah ya tsinewa mutumin da ya jagoranci mutane alhalin ba sa sonsa.

Don haka ne ma imam Ali (A.S) ya ki jagoranci saboda mutane ba su zabe shi ba, amma da suka zabe shi ya riki mulki kuma da wani ya tashi domin ya kwata daga gareshi sai ya yake shi da mutanen.

Mulki a hannun bayin Allah (S.W.T) nagari da ya zaba ita ce hanyar shiryar da bayi, don haka idan suka ki Allah madaukaki bai yarda a tilasta su ba. Amma kuma idan mutane suka ki yarda da zabin Allah (S.W.T) -duk da Allah ya kyale su bai yarda a tilasta su karbar wanda ba sa so ba- amma bala’o’in duniya da na lahira zasu durfafe su.

Mu duba mu gani mana a lokutan jagorancin manzon rahama (S.A.W) da imam Ali (A.S) ba a taba samun wani ya mutu da yunwa ko talauci ba, kuma ba a samu yawaitar jahilci da rashin tsaro ba, kuma ba a samu karancin abinci da yunwa ba saboda tsarin da suka zo da shi a hukumarsu duk da kuwa kowannensu hukumarsa cike take da yake-yake!

Muna iya gani abin da imam Ali (A.S) ya yi yayin da ya ga wani tsohon bayahude a hanya a Kufa yana bara sai ya tambaya ya ce: me ye haka! Mu duba mu gani bai ce wane ne wannan ba, sai ya ce mene ne wannan, wato bakon abu ne a daularsa a samu bara. Sai ya yi fada kan cewa; wannan bayahuden ya yi wa mutane ayyuka yana saurayi sai da ya tsufa sannan sai a kyale shi!? sannan ya sanya masa albashi daga Baitul mali!



back 1 2 3 4 5 6 7 next