Tsarin Siyasa A MusulunciTsarin Siyasa A Musulunci
Dandalin Siyasa
Mece Ce Siyasa?
Wasu Suna Cewa: Siyasa a dunkule ta kunshi jagorancin al’umma da tsarin tafiyar da al’amuransu (da yake cikin tsarin da dan’Adam yake a kansa a kasashe da ya hada da majalisar dokoki da ta yin doka (kotu) da ta zartarwa (wacce ministoci da shugaba suke cikinta). Ashe kenan muna iya cewa jagorancin al’umma a dunkule shi ne ake nufi da siyasa, kamar yadda kalma ce ta larabci da take nufin jagorancin al’umma da tafiyar da al’amuransu. Kodayake kada mu manta da yadda ake amfani da wannan kalmar da ma’anar yaudara, ko kuma sanya bangaranci a cikin warware wasu al’amura ko kuma kushe wani abu da ya fito ba daga namu bangaren ba, da makamantan hakan. Idan kana son ka gane hakan sosai duba yadda zabe yake a kasashenmu na Africa da yadda yake gudana, kai idan ina son in kawo misali duba ZIMBABWE a wannan kwanakin ka ga me yake gudana na tsananin zaluncin shugaba da neman mulki hatta da karfin tsiya, irin wadannan al’amuran duk ana kiransa siyasa musamman da yake ya shafi lamarin tafiyar da al’amuran al’umma koda kuwa ta kowace hanya ce. Kuma kungiyoyin da suke neman kaiwa ga wannan matsayin na rike ragamar tafiyar da kasa ana kiransu kungiyoyin siyasa. A nan ne fa aka fara maganar cewa; shin siyasa wani bangare ne na addini ko kuma wani abu ne daban da ba shi da alaka da addini? Kuma shin addini yana da wani matsayi da ya dauka a kan siyasa ko kuwa? A nan ne fa aka fara maganar cewa; shin siyasa wani bangare ne na addini ko kuma wani abu ne daban da ba shi da alaka da addini? Kuma shin addini yana da wani matsayi da ya dauka a kan siyasa ko kuwa? Idan mun duba tarihin rayuwar dan’Adam tun farkon samuwarsa yana tare da siyasa ne, sai mutum na farko ya kasance shugaba da zabin Allah a kan zuriyarsa, sai ya kasance annabi ne da yake karbar sako daga Allah (S.W.T) kai tsaye domin ya shiryar da shi kan yadda zai tafiyar da al’amuran jama’a a duniya, kai wani tunani da ya zo mini a kwakwalwata da na dade ina mamakinsa shi ne; cewar Allah (S.W.T) a farkon maganarsa game da dan’Adam da zai halitta ya fara ne da maganar siyasa yayin da yake gaya wa mala’iku cewa; zan sanya halifa a duniya. Halifa kuwa yana nufin mai maye gurbin Allah (S.W.T) a kowane abu a duniya da ya hada da tafiyar da al’amuran bayi wanda shi ne bangare mafi muhimmanci, domin kuwa shi ne ya shafi shiryar da dan’Adam kan al’amuransa na duniya da lahira. Duba ka gani yayin da Allah (S.W.T) ya ce da mala’iku: “Ni mai sanya halifa (mai wakiltata) a bayan kasa ne…†Bakara: 30. Da fadinsa: “Ya kai Dawud mu mun sanya ka halifa (mai wakiltar Allah cikin tafiyar da al’amuran bayi) a bayan kasa, sai ka yi hukunci tsakanin mutane da adalci…†surar Saad: 26. Da wannan ne zamu iya gane cewa tun farko addini yana damfare da siyasa kai tsaye, kuma tushen addini ya kafu kanta koda kuwa wasu daga malaman musulmi sun ki yarda da hakan. Amma dayawan ruwayoyi sun nuna mana ba yadda za a yi a cire jagoranci daga tushen addini, don haka imani da jagorancin annabawa (A.S) da kuma wasiyyoyi da wasiyyai (A.S) da suka bari yana daga tushen addini, kuma idan mutum bai yi imani da su ba koda kuwa ya fi kowa biyayya ga Allah a sauran bangarori Allah ba zai karbi ibadarsa ba, don haka ne ma duk wanda ya mutum bai san jagoran zamaninsa ba to ya yi mutuwar jahiliyya. (Minhajul karama, Allama Hilli, Shafi: 27). Domin zai zo a lahira babu wani abu da Allah zai karba na ayyukansa. Don haka yarda da manzon Allah (S.A.W) da wasiyyoyinsa da wasiyyansa (A.S) wanda ya hada da Kur'ani da halifofinsa (A.S) wadanda bai bar mutane ba sai da ya gaya musu wadannan halifofin nasa kuma ya fadi adadinsu cewa su sha biyu (A.S) ne kuma ya fadi sunanyensu sannan kuma Manzon Allah mai tsira da aminci ya gaya wa mutane ba zasu taba kauce wa hanya ba suna tare da Kur'ani har sai sun riske shi a tafkin alkausara a ranar lahira. Ashe kenan siyasa ita ce tushen addini da idan ma ba ka zama dan siyasa ba karkashin jagorancin da Allah (S.W.T) ya gindaya maka to kai ayyukanka ba zasu karbu ba har abada, zaka yi mutuwar jahiliyya ne. Don haka ne ma halifan manzon Allah (S.A.W) da ya yi wasiyya da shi na farko kuma jagoran Ahlul-bait (A.S) ya tambayi manzon Allah (S.A.W) bayan ya gaya masa kamar yadda al’ummar annabi Musa (A.S) da Isa (A.S) ba su bi wasiyyansu ba shi ma al’ummar nan ba zata bi shi ba, ya tambayi manzon Allah (S.A.W) cewa; zan yi wa al’ummar nan hukuncin kafirai ne ko kuma hukuncin wadanda suka fada fitina? Sai manzon Allah (S.A.W) ya amsa masa ya yi musu hukuncin wadanda suka fada fitina ne. Wannan kuwa lallai fitina ce, domin babu bala’in da ya kai ga cewa; Allah ba zai karbi duk ibadojin mutum ba!! A nan ne zamu samu natijar amsar tambayarmu cewa; shin addini yana tare da siyasa. Don haka muna iya gani cewa; asali ma tushensa ya doru ne kan siyasar.
|