Hadisan AnnabiDA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI
Yana daga cikin abinda mazahabin Ahlul Baiti (A.S) ya kebanta da shi girmama hadisan Wasiyyan Manzo Bayan hadisan Manzon (S.A.W) domin hadisansu sun kasance daga hadisansa ne, wato kamar yadda hadisansa suke fassara Alkur’ani haka ma hadisansu da umarnin Manzo (S.A.W) na a yi riko da su da kuma Alkur’ani bayansa (S.A.W) . Sa’annan falaloli da dama sun zo akan hardace hadisai arba’in don haka wadannan hadisai arba’in da ‘yan kai mun tanade su muka zuba su a nan domin neman albarkar wancan hadisi da kuma fatan a hardace su a kiyaye su a kuma yi aiki da su. قال رسول الله صلّى الله عليه Ùˆ آله : Ù…ÙŽÙ† أصلَØÙŽ Ùيما بَينَه٠وبَينَ الله٠أصلَØÙŽ الله٠Ùيما بَينَه٠وبَينَ النّاسÙ. Manzon Allah (S.A.W) ya ce : Duka wanda ya gyara tsakaninsa da Allah to Allah zai gyara masa tsakaninsa da mutane. قال رسول الله صلّى الله عليه Ùˆ آله: خَÙ٠اللهَ كَأَنَّكَ تَراه٠ÙÙŽØ¥ÙÙ† ÙƒÙنتَ لاتَراه٠ÙÙŽØ¥Ùنَّه٠يَراكَ . Manzon Allah (S.A.W) ya ce : Ka ji tsoron Allah kamar kana ganinsa idan ka kasance ba ka ganinsa ai shi yana ganinka. قال Ùاطمه زهراعليها السّلام: Ù…ÙŽÙ† أصعَدَ إلَى الله٠خالÙصَ عÙبادَتÙÙ‡ Ùأهبَطَ الله٠إلَيه٠أÙضَلَ مَصلَØَتÙÙ‡ FatimatuzZahra (AS) tana cewa: Duk wanda ya kusanta da Allah yana mai tsarkake ibadarsa Allah zai saukar masa da mafificiyar maslaharsa (ya biya masa mafificiyar bukatarsa)
|