Sahifatus Sajjadiyya



Da kuma misalin addu'a ta 28:

"Ya Allah ni na tsarkake niyyata gare ka duka, kuma na juyo zuwa gare ka baki daya, kuma na juyar da fuskata daga dukan ma'abucin taimakonka, Na juyo da al'amarina daga dukan wanda ba zai taba wadatuwa ya bar falalarka ba, kuma na gane cewa bukatar mabukaci zuwa ga wani mabukacin wautar ra'ayinsa ne kuma bacewar hankalinsa ne."

Kazalika addu'a ta 13:

"Duk wanda ya yi kokarin magance rashinsa ta gurinka kuma ya yi kokarin raba kansa da talauci da taimakonka to lalle ya nemi abin bukatarsa a gurin da ake tsammani, kuma ya zo wa bukatarsa ta gurin da ake tsammani, kuma ya zo wa bukatarsa ta gurin da ya dace Kuma duk wanda ya juya da bukatarsa kuwa ga daya daga cikin halittunka, ko kuma Ya sanya shi sababin cimmata ba kai ba to lalle ya jawo wa kansa hani kuma ya cancanci kubucewar kyautatawa daga gare ka."

Na Shida:

Koya wamutane wajabcin kiyaye hakkokin wasu, da taimaka musu da tausasawa gare su, da rangwame ga junansu, da sadaukarwa da tabbatar da ma'anar yan'uwantakar musulunci, kamar yadda kake karantawa a addu'a ta 38:

"Ya Allah niina mai neman uzuri daga gare ka a kan dukan wani da aka zalunta a gabana amma ban taimake shi ba, da kuma wani kyakkyawan abu da aka kwararo mini shi amma ban yi godiyarsa ba. da kuma duk wani mabukaci da ya roke ni amma ban ba shi ba, da kuma daga hakkin duk wani ma'abucin hakki da ya hau kaina daga muminai amma ban cika mashi ba, da kuma daga dukan wani aibi na mumini da ya bayyana gare ni amma ban suturce shi ba."

Lalle wannan irin neman uzuri yana daga cikin mafi bayyanar abinda zai fadakar da zuciya zuwa ga abinda aikata shi ya kamata na wadannan kyawawan dabi'u madaukaka da ubangiji ya yarda da su.

A addu'a ta 39 akwai abinda ke ba da karin haske a kan haka tare da lizimtar da kai yadda za ka yale wa wanda ya munana maka yana kuma gargadinka game da yin ramuwar gayya yana kuma daukaka zuciyarka zuwa matsayin tsarkakuwa:

Ya Allah duk wani bawa da Ya cutar da ni da wani abu da ka haramta, kuma ya keta mini abinda ka riga ka hane shi a kai, kuma ya mace da zaluntata ko kuma Ya auku a kaina daga gare shi Yana rayayye to ka gafarta masa abinda ya yi mini ka yafe masa abinda ya riga ya aukar Ya wuce daga gare ni, kada ka dakatar da shi da tambaya a kan abinda ya aikata a kaina, kuma kada ka tona asirinsa a kan abinda ya aikata a kaina, kuma ka sanya rangwamen da na yi masa na afuwa gare su da kama sallamawar da na yi musu na daga sadaka gare su ya zama sadakar masu sadaka, kuma mafi kololuwar sadarwar ma'abuta kusanci gare ka. Kuma ka musanya mini afuwata gare su da afuwarka, da kuma addu'ata gare su rahamarka, har ya zamanto kowane daya daga cikinmu ya rabonta da falalarka ya kuma samu tsira saboda baiwarka."

Al 'ajabin wannan yankin addu'ar da yawa yake, kyawun tasiri da shigarta zuciyar zababbu Yayawaita, don fadakar da su a kan Lizimtar kyakkyawar niyya da dukkan mutane, da neman rabauta ga kowa da kowa hatta ma wanda Ya zalunce shi ya ketare masa haddi.

Hafizu Muhammad Sa’id Kano Nigeria.

 

 



back 1 2 3 4 5