Sahifatus Sajjadiyya



Da kuma wadda kake karantawa a addu'a ta 39:

"Domin kai idan har ka saka mini daidai wa daida to za ka halakar da ni Idan kuma ba ka lullube ni da rahamarka ba to za ka halakar da ni Kuma ina rokon ka ka dauke daga zunubina wanda nauyinsa ya dankare ni Kuma ina neman taimako da kai a kan abinda nauyinsa Ya riga ya makure ni. Don haka ka yi dadin tsira ga Muhammadu da zuriyarsa Kuma ka ba wa raina kansa saboda zaluncinsa ga ni kaina, kuma ka wakilta rahamarka wajen daukar nauyina."

Na Hudu:

Jan mai addu'a zuwa ga madaukakan matsayin ayyuka da kebantattun siffofi domin kyautata ruhinsa da tsarkake zuciyarsa ta

hanyar karanta wannan addu'ar kamar yadda kake karantawa a addu'a ta 20:

'`Ya Allah ka kammala min niyyata da tausasaawarka, kuma ka inganta mini niyyata da abinda ke gare ka. kuma ka gyara mini abinda ya baci daga gare ni da kudurarka, ...Ya Allah ka yi dadin tsira ga Muhammadu da zuriyar Muhammadu ka jiyar mini dadi daga shiriya ingantacciya wadda ba zan taba neman musayenta ba, da kuma hanya ta gaskiya wadda ba zan taba karkacewa daga kanta ba, da kuma niyyar shiriya da ban taba kokwanto a kanta ba.

... Ya Allah kada ka bar wani hali da yake aibi gare ni face ka gyare shi, ko kuma wani laifi da za a zarge ni da shi illa ka kyautata shi. Ko kuma wani halin karimci da yake tauyayye gare ni har sai ka cika Shi."

Na biyar:

Sanya wamai karanta addu'ar mutunta mutane da rashin kaskantar da su, da kuma cewa kada ya sanya bukatarsa a gurina wani ba Allah ba. da kuma cewa kwadayin abinda ke hannun mutune na daga cikin ma  kaskancin abinda mutum zai siffantu da shi kamar wadda kake karantawa a addu'a ta 20:

"Kuma kada ka fitine ni da nema:: taimakon wani ba kai ba idan na matsu da kuma kankan da kai don tambayar wani ba kai       ba, idan na bukata, da kuma mika wuya gaba ga wanda ba kai ba idan na tsorata, kada na zamanto na tozarta da hanawa da kau da kai ta yin haka."



back 1 2 3 4 5 next