Sahifatus Sajjadiyya



Daga cikinsu akwai wadanda ke maka sharhin wajiban sojojin musulunci da wajiban mutane dangane da su... da dai sauran wadannan da kyawawan dabi'u abin yabo suke farlanta su, duk ta hanyar addu'a kawai.

Bayyanannun al'amuran da ke fitowa a fili a addu'o'in Imam sun kasu kamar haka:-

Na farko: Sanin Allah Ta'ala da girman kudurarSa da bayanin kadaita Shi, da tsarkake shi, da mafi dacewar ma'anoni na ilimi, wannan kuwa yana maimaituwa ne a kowace addu'a ta salo daban-daban kamar yadda kake karantawa a addu'a ta farko :

"Godiya ta tabbata ga Allah na farko w-anda babu wani na farko da Ya kasance kafin shi na karshen da babu wani na karshe da zai kasance baicin Shi wanda idandunan masu gani suka gaza ganin sa. wahamce- wahamcen masu sifance - sifance kuma suka gajiya wajek siffanta Shi. Ya fari halittu da kudurarSa a farko farawa Ya kuma kago su kamar yadda ya so kagowa."

Karanta ma'ana ta farko da kyau kuma ka yi tunani a kanta zaka tsarkake Allah Ta'ala daga kasancewarsa wani ya zamanto Ya gewaye da gani ko da wahami, da kuma ginin ingancin ma'anar halitta da kuma halittar duniya baki daya. Daga nan kuma ka karanta wani salon wajen bayyana kudurar Allah "ta'ala da yin tuntuni a addu'a ta 6:

"Godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya halitta dare da rana da karfinSa,Ya rarrabe tsakaninsu da kudurarsa,Ya sanya ga kowane daga cikinsu su biyun iyaka ayyananniya, Yana shigar da kowane daya daga cikinsu a cikin dan'uwansa a cikinsa da kaddarawarsa ga bayi a cikin abinda yake ciyar da su kuma yake sanya su su girma. Don haka Ya halitta musu dare ne domin su huta wahalar kaiwa da komowa da dawainiya kuma Ya sanya shi sutura da za su suturtu da kwanciyarsu da natsuwarsa domin hakan ya zama musu wartsa kewa da kara samun kari kuma domin su kara samun jin dadi da sha'awa har zuwa karshen abubuwan da ya ambata na fa'idar halittar rana da dare da kuma abinda Ya kamata mutum Ya yi godiyarsa daga wannan ni'imar.

A wani salon kuma na bayanin dukan al'amura ga Allah Ta'ala suke za ka karanta a addu'a ta 7 cewa:

"Ya wanda da Shi ne kulle-kullen munanan abubuwa ke suncewa, Ya wanda da shi ne Kaifin tsanani ke duskurewa, ya wanda daga gare Shi ake rokon mafita zuwa tsantsan sauki mawuyatan al'amura na rusunawa ga kudurarka, sabubba kuma sun samu ne da tausasawarka, kaddarawarka kuma ta gudana ne a bisa iradarka, su da iradarka suke bin umarninKa, kuma masu umartuwa da maganarka ne kuma da iradarka ne suke tsawatuwa da haninKa."

Na Biyu:

Bayani game da falalar Allah ga bawansa, da kuma gazawar bawa wajen bayar da hakkin Allah Ta'ala kome abinda Ya yi na da'a da ibada kuwa da kuma yankuwa don juyawa ga Allah kamar yadda kake karantaw-a a addu'a ta 37:



back 1 2 3 4 5 next