Sahifatus Sajjadiyya



"Ya Allah Lalle babu wani da zai kai ga matukar godiya gare ka face wata Kyautatawarka ta same shi wadda za ta sake lizimta masa wata godiyar. Kuma ba ya kaiwa ga matukar da'arka koda kuwa ya dage face ya gaza yin yadda ka cancanta a kan falalarka, Mafificin mai godiya gare ka a bayinka ya gaza a kan godiyarKa, kuma mafi bautarsu mai kwauro ne a bautarKa."

Saboda girman ni’imomin Allah ta’ala kan bawansa bawan ya yi kadan ya ba da hakkinsa komai kokarin da ya yi kuwa.

To yaya kuma idan har Ya sabe shi yana mai tsaurin kai, yayin nan kuma ba zai taba iya kankare sabo koda guda daya ba, kuma wannan Shi ne abinda yankin addu'ar da ke biye a addu'a ta16 ke nunawa:

"Ya Ubangijina idan da zan yi kuka har fatar idona ta zagwanye, kuma na yi kururuwa har muryata ta dushe, kuma na tsaya gare ka har kafafuwana su tsattsage kuma na yi maka sujada har kwayar idandunana su faffado, kuma na ci turbayar kasa duk tsawon rayuwata kuma na sha ruwan toka har zuwa karshen zamanina sa'an nan na yi ta ambaton ka duk tsawon wannan lokacin har sai harshena ya gaza, sa'an nan kuma na zama ban taba daga ganina na dubi sama ba don jin kunyar ka, duk wannan ba zai wajabta shafe mini mummunan aiki daya daga miyagun ayyukana ba."

Na uku:

Sanar da lada da ukuba da aljanna da wuta da kuma cewa ladan Allah dukkaninsa kyauta ne kawai kuma bawa ya cancanci a zaba ne da zarar aikata sabo guda daya kawai da ma  tsaurin idon aikatawa, Kuma Allah na da hujja a kansa game da haka.

Kuma dukan addu"o'in Sahifatus Sajjaddiya ta ambata wannan Ukubar mai tasiri domin samar wa zuciya tsoron ukubar Allah ta'ala da sanya mata sa tsammani da ladan Allah Ta'ala. Dukkanta shaida ce a kan haka ta salo mafifici da ke sa wa zuciya mai tuntuni tsoro da firgita kan kama hanyar Sabo, wato kamar abinda za ka karanta a addu'a ta 46:

"Hujjarka tabbatacciya ce ba za ta shafu ba, Shugabancinka tsayayye ne ba ya ciruwa, don haka tsananin azaba Madawwami ya tabbata ga wanda ya nisance ka, tabewar tozartuwa ta tabbata ga wanda ya karkace daga gare ka, tsiyacewar tsiyata ta tabbata ga wanda Ya rudu Ya bar ka, jujjuyawarsa a azabarka ta yawaita, taraddudinsa a cikin ukubarka Ya ya waita, bukatarsa ga samun budi ta kai matuka, debe tsammaninsa ga samun mafita mai sauki Ya tsawaita, Adalci ne daga hukuncinka ba ka zalunci a cikinsa, da kuma yin daidai a hukuncinka ba ya kaucewa, lalle ka bayyanar da hujjoji kuma ka jarraba uzurori."

Da kuma kamar yadda kake karanta addu'a ta 31.

"Ya Allah ka ji kan kadaitakata a gabanka, da kidimewar zuciyata daga tsoronka da firgicewar gabobina don haibarka, kuma lalle Ya Ubangijina zunubina Ya sanya ni a matsayin kaskanci a gurinka. Idan har na yi shiru babu wani da zai yi magana madadina, idan kuma na nemi a cece ni to ni ban cancanci ceto ba."



back 1 2 3 4 5 next