Sahifatus Sajjadiyya



Sahifatus Sajjadiyya

Bayan aukuwar al'amarin karbala mai ban takaici da kuma kame ragamar shugabancin al'ummar musulmi da Banu Umayya suka yi kuma suka dulmuya a cikin danniya suka yi dumu-dumu da jinin mutane sa'an nan suka yi watsi da koyar war addini sai Imam Zainul Abidin (A.S.) wato Sayyiddus Sajidin Ya zauna a gidansa yana bakin ciki da jin takaici. Yana gida babu wani mai kusatarsa kamar yadda ba zai iya yada wa mutane abinda Ya wajaba a kansu ko ya kamata su sani ba na addini, don haka ala tilas ya zama babu makawa gare shi ya dauki salon addu'a wanda muka ambata da cewa yana daga cikin hanyoyin koyarwa da ladabtar da zukata ya rike shi a matsayin hanyar yada koyarwar Alkur'ani da ladubban musulunci da kuma sanar da tafarkin Ahlul Bait (A.S.) da kuma hanyar cusa wa mutane ruhin addini da zuhudu da kuma abinda ya wajaba na daga gyaran zukata da kuma kyawawan dabi'u.

wannan hanya ce da ya fare ta a fakaice don koyar wa mutane ba tare da ya jawo hankalin azzaluman Shugabanni da ke matsa masa ba. ba kuma za su iya kafa masa wata hujja ba. Don haka ne yawancin wadannan addu'o'i masu zurfi an tattara wadansunsu a littafin Sahifatus Sajjadiyya wanda ake yi wa lakabi da Zaburar Zuriyar Muhammadu(SAW) salonta da manufofinta sun zo da siga da salon Larabci mafi daukaka, da mafi ingancin asirran tauhidi da Annabci da kuma mafi ingancin hanyar koyar wa da kyawawan dabi'u ababan yabo da kuma ladubban musulunci.

Wadannan addu"o'in sun shafi al'amura daban-daban ne na tarbiyya ta addini da ta shafi koyarwar addini da kyawawan dabi'u ta hanyar addu'a, ko kuma addu'a ce amma da salon koyar da addini da kuma kyawawan dabi'u. Alal hakika bayan Alkur'ani da Littafin Nahjul Balagha wannan Littafin addu'o'in Shi ne salon bayanin Larabci mafifici kuma mafi daukakar mashayar manufar sanin ubangiji da kyawawan dabi'u. Daga cikinsu akwai wandake sanar da kai yadda zaka daukaka Allah kuma ka tsarkake shi, kana kuma ka yi hamdala ka yi wa Allah godiya, daga bisani ka tuba gareshi.

Daga ciki akwai wadda ke sanar da kai yadda zaka yi zance da Allah, kuma ka kadaita da kai da ubangijinka kana mai bayyana masa asirinka sannan ka zabura zuwa gare shi.

Daga cikinta akwai wadanda ke shimfida maka ma'anar Salati ga Annabi (SAW) da Manzannin Allah da zababbunsa daga cikin halittunSa dayadda za ka yi da Shi.

Daga cikinsu akwai wadanda za su fahintar da kai abinda ya dace ka bi iyayenka da shi.

Kazalika akwai wadanda ke maka sharhin hakkokin Uba a kan dansa, ko kuma hakkokin makwabta, ko wadanda kuke ciki daya, ko hakkokin musulmi baki daya, ko hakkokin matalauta a kan mawadata da kuma akasin haka.

Daga cikin addu'o'in akwai wanda zai fadakar da kai kan abinda ya wajaba na basussukan mutane akan ka, da kuma abinda ya kamata ka aikata akan lamurran kafi da tattalinsu, haka na da abinda ya kamaia kayi mu'amala da shi tsakaninka da masu hulda da kai da sauran abokanka da kuma mutane baki daya, har yanzu akwai wanda zai gwada maka irin mutanen da za ka iya hulda da su domin amfanin kanka.

Daga cikinsu akwai wadanda suke hado maka dukan manyan halayen kwarai da za sa su iya zama cikakken tsari na ilimin kyautata dabi'u.

Daga cikinsu akwai wadanda za su koya maka yadda za ka yi hakuri a kan munanan abubuwa da ke aukuwa da kuma yadda za ka yi yayin da kake ciwo da kuma yayin da kake kalau.



1 2 3 4 5 next