Mu’amala ta Musamman



Ko kuma magance masa matsaloli da bakin cikin da ke ciki, daga Zaid al-Shaham yana cewa: Na ji Aba Abdillah (a.s) yana cewa: “Wanda ya taimaka da fitar da dan’uwansa mumini daga bakin cikin da ke ciki, da taimaka masa wajen biyan bukatunsa, Allah Madaukakin Sarki zai rubuta masa rahama saba’in da biyu saboda wannan aiki nasa, zai gaggauta masa guda daga cikinsu wajen kyautata lamurran rayuwarsa, sauran saba’in da dayan kuma zai ajiye masa su don tseratar da shi Ranar Kiyama da wahalhalun da ke cikinta[17]”.

Ko kuma wasun hakan na daga cikin mu’amaloli irin su hada kai da shi, taimakonsa da yi masa nasiha.

Makwabta

f) – Haka nan mu’amala ta musamman da makwabta, da a baya muka yi magana kanta, cikakken karin bayani kan hakan na cikin hukumce-hukumce goma. A nan za mu yi ishara ne da wasu hadisai kamar yadda muka yi alkawari.

1- Daga Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: Kyautata makwabtaka na raya gidaje………..[18]”.

Daga Abi Mas’ud yana cewa: (wata rana) Abu Abdullah (a.s) ya ce min: “Kyautata makwabtaka kari ne ga shekaru (rayuwa), kana kuma gyara ne ga gida[19]”.

Abu Rubai’ al-Shami yana cewa Abu Abdillah (a.s) ya ce: alhali gida na kokarin nutsewa da masu shi: “Ku sani cewa ba ya daga cikinmu wanda bai kyautata makwabtaka ga wanda ya kasance makwabcinsa[20]”.

2- Daga Abi Ja’afar (a.s) yana cewa: “Iyakan makwabtaka shi ne gidaje arba’in daga kowace kusurwa, daga gabansa, daga bayansa, daga damansa da kuma daga hagunsa[21]”.

3 – Daga Umar bn Akrama daga Abi Abdillah yana cewa: “Wani mutum daga cikin Ansar (mutanen Madina) ya zo wajen Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce masa: Na sayi wani gida daga wajen kabila kaza, sai dai makwabcin da ya fi kusanci da ni wani mutum ne da ba na zaton alherinsa ko kuma amintaka daga sharrinsa. Sai ya ce: sai Manzon Allah (s.a.w.a) ya umarci Aliyu da Salman da Abu Zar, na mance daya mutumin amma ina zaton Mikdad ne, da su daga sautinsu iyakacin iyawansu ciki masallaci da cewa babu imani ga wanda ke cutar da makwabcinsa, sai suka fadi hakan har sau uku, daga nan sai ya yi ishara da hannayensa zuwa ga gidaje arba’in daga gabansa, da bayansa, dama da hagunsa[22]”.

4- Daga Hasan bn Abdillah daga Abdussahlih yana cewa: “Kyautata makwabtaka ba shi ne rashin cutarwa ba, face kyautata makwabtaka ita ce hakuri kan cutarwa[23]”.

Daga Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “……………, mai yiyuwa ma dukkan uku su hadu masa: imma dai o wasu daga cikin wadanda yake tare da su suna rufe masa kofa don cutar da shi, ko kuma makwabcin da ke cutar da shi, ko kuma wanda suke tare da shi wajen biyan bukatunsa yana cutar da shi. Da wani mumini zai kasance a koluluwar dutse da Allah Madaukakin Sarki Ya aike masa da wani shaidani ya cutar da shi,……..[24]”.



back 1 2 3 4 5 next