Mu’amala ta Musamman



Na Biyar: Ma’aunin Mu’amala ta Musamman

A nan za mu iya samun karin bayani da yawa da aka ambata cikin babuka da maudhu’ai daban-daban na fikihu da shari’a da za a iya samunsu a wajajen da suka dace, amma duk da haka, a nan bari mu yi ishara da wasu misali da aka kawo su cikin babuka da dabi’u guda goma, bugu da kari kan abubuwan da aka yi ishara da su a baya, ko kuma wadanda za mu iya samunsu cikin ka’idoji da asasai na alaka ta zamantakewa. Duk da cewa an iyakance su, amma duk da haka suna da amfani a bangare na nazari kan wadannan batutuwa:

Salatiga Iyalan Manzo

a) – Batun salati ga Manzon Allah da Iyalansa a ko ina a kuma kowani irin yanayi – kamar yadda za mu ishara da shi a tsarin alamomi da ibadu nan gaba – na nuni da irin wannan kebantacciyar mu’amala, ta yadda hatta za mu iya ganin cewa gabatar da salatin Manzo da Iyalansa a kan addu’a yana a matsayin dalilin karbuwar addu’ar. Saboda Allah Madaukakin Sarki ba ya mayar da addu’ar da aka yi salati a gabanninta, saboda karimcinSa zai sa Ya karbi addu’ar da rashin dawo da ita, kamar yadda aka ruwaito hakan wajen Amirul Muminina (a.s) inda yake cewa: “Idan kana da wata bukata wajen Allah Madaukakin Sarki, to ka fara da salati ga ManzonSa (s.a.w.a) kana ka roki abin da kake so, saboda karimcin Allah ya fi karfin a tambaye Shi bukatu biyo ya biya guda ya yi watsi da guda[1]”.

Kamar yadda yana da kyau mutum ya hada gode wa Allah (fadin alhamdu lillah) yayin atishawa da salati ga Manzo da Iyalansa, kai face ma dai a dukkan yanayi ko da kuwa na musamman ne, don ba da muhimmanci ga wannan mu’amala ta musamman.

Daga Ibn Abi Umair, daga wasu sahabbansa, yana cewa: wata rana wani mutum ya yi atishawa wajen Abi Ja’afar (a.s) sai ya ce: alhamdu lillahi amma Abu Ja’afar (a.s) bai amsa masa ba (wato bai nema masa gafara kamar yadda ake yi wa wanda ya yi atishawa ba), sai ya ce: “Mun rage hakkinmu”, ya ce: “Idan waninku ya yi atishawa, sai ya ce: alhamdu lillahi Rabbil alamin wa sallallahu ala Muhammad wa Ahli baitihi –godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Muhammad da Iyalan gidansa –”, sai mutumin ya fadi hakan sai Abu Ja’afar ya amsa masa[2].

Cikin wasikar Imam Ridha (a.s) ga Ma’amun, Imam yana cewa: “Salati ga Annabi (s.a.w.a) wajibi a ko ina, a lokacin atishawa da yanka da sauransu[3]”.

KyautatawaGa Zuriyar Annabi

b) – Baya ga wannan, akwai hadisai da yawa da aka ruwaito daga wajen Manzon Allah (s.a.w.a) ta hanyar Ahlulbaiti (a.s) da ke jaddadawa kan mu’amala ta musamman ga Zuriyar Manzo na daga alawiyyawa da sayyidai (sharifai), ta hanyar kyautatawa da girmama su.

Daga Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: wanda ya sana’anta hannu ga daya daga cikin zuriyata, za a saka masa da shi Ranar Kiyama[4]”.

Daga gare shi yana cewa: “Idan Ranar Kiyama ta tsaya, wani mai kira zai yi kira da cewa: Ya ku halittu! Ku yi shiru, Muhammadu (s.a.w.a) na da magana, dukkan halittu za su yi shiru, sai Annabi (s.a.w.a) ya mike ya ce: Ya ku halittu! Duk wanda ke da wani taimako, ko korafi ko kuma kyakkyawan aiki gare ni, ya mike in saka masa. Sai su ce: Mun rantse da iyayenmu maza da iyayenmu mata, wani taimako ko korafi ko kyakkyawan aiki muke da shi? face dai taimako, korafi ko kyakkyawan aiki na Allah da ManzonSa ne kan dukkan halittu, sai ya ce musu: lalle haka ne, shin akwai wanda ya kula (taimakawa) da guda daga cikin zuriyata, ko kuma ya kyautata musu, ko kuma ya suturce su daga huntanci (tsiraici), ko kuma ya ciyar da mai jin yunwansu, ya tashi in saka masa, sai mutanen da suka aikata hakan su mike, sai aji wani kira daga wajen Allah Madaukaki: Ya Muhammadu! Ya abin kaunata! an sanya sakayyarsu ga hannunka, ka sanya su cikin Aljanna yadda ka ke so. Sai ya ce: zai sanya su kan tafarki, ta yadda ba za a kange su daga Muhammadu da Iyalansa (a.s) ba[5]”.

Daga Imam Ridha (a.s) daga Iyayensa yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: Zan ceci mutane hudu Ranar Kiyama: mai kyautatawa ga zuriyata a bayana, mai biya musu bukatunsu, mai kokari gare su wajen magance musu matsalolin da suke ciki da kuma mai kaunarsu da zuciya da harshensa[6]”.

Daga Imam Bakir (a.s) daga babansa daga kakansa (a.s) yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: wanda ke son isa gare ni, kuma yake son in ceci shi Ranar Kiyama, to ya isa (taimakawa) ga Mutanen gidana da sanya musu farin ciki[7]”.



1 2 3 4 5 next