Mu’amala ta Musamman



Daga Imam Bakir (a.s) yana cewa: “Idan kiyama ta tsaya, Allah Zai tara na farko da na karshe, sai mai kira ya ce: wanda ke da hannun (taimako) ga Manzon Allah (s.a.w.a) ya mike tsaye, sai wasu jama’a su mike, sai ya ce musu: mene ne taimakonku ga Manzon Allah (s.a.w.a)? sai su ce: mun kasance mukan taimakawa zuriyarsa a bayansa, sai a ce musu: ku zagaya cikin mutane, ku dauki duk wani wanda ya taimaka muku zuwa Aljanna[8]”.

Tsoffi(Dattijai)

c) – Girmama tsoffi da dattawa ma’abuta shekaru masu yawa na nuni da mu’amala ta musamman ga wadannan nau'i na mutane ma’abuta rauni.

Daga Abdullah bn Sanan yana cewa: Abu Abdullah (a.s) ya ce min: “Girmama dattijo mai yawan shekaru na daga cikin girmama Allah Madaukakin Sarki[9]”.

Daga gare shi (a.s) yana cewa: “Ba ya daga cikinmu wanda ba ya girmama mai yawan shekarunmu sannan kuma ba ya tausayawa karaminmu[10]”.

Mahaddacin Alkur’ani

d) – Girmama mahaddacin Alkur’ani a matsayinsa na masanin addini da shari’a, kuma mai isar da sakon Allah kuma mai karanta ayoyin Ubangiji.

Abu Abdullah (a.s) yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: Ma’abuta Alkur’ani suna da matsayi mai girma da daukaka cikin mutane in banda Annabawa da Manzanni, don haka kada ku tauye wa ma’abuta Alkur’ani hakkokinsu, saboda suna da matsayi a wajen Allah Madaukakin Sarki[11]”.

Mumini

e) – Haka nan mu’amala ta musamman da mumini[12], da suka hada da sanya masa farin ciki. An ruwaito hakan cikin wasu ingantattun hadisai, misali abin da Kulayni ya ruwaito daga Abi Hamza al-Thumali yana cewa: Na ji Aba Ja’afar (a.s) yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: wanda ya faranta wa mumini rai ya faranta mini rai ne, wanda ya faranta min kuwa ya faranta wa Allah rai ne[13]”.

Daga Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Sanya farin ciki (cikin zuciyar) mumini na daga cikin ayyukan da suka fi soyuwa wajen Allah Madaukakin Sarki; kosar da shi daga yunwarsa, magance masa wahalar da ke ciki ko kuma biyan bashin da ke kansa[14]”.

Ko kuma biyan bukatar mumini, kamar yadda aka ruwaito daga Abi Abdillah (a.s) yana cewa cikin wani hadisi: “Wanda ya biya wa dan’uwansa mumini bukata, Allah Madaukakin Sarki Zai biya masa bukatunsa guda dubu dari a Ranar Kiyama, na farko daga cikinsu shi ne Aljanna, daga ciki kuma har da za a shigar da makusantansa, wadanda ya sansu da ‘yan’uwansa Aljanna bayan da ba su cancanci hakan ba[15]”.

Daga Abi Ja’afar (a.s) yana cewa: “…………[16].”.



back 1 2 3 4 5 next