Hadiye Fushi da Juriya



An ruwaito cikin wani hadisi daga Abi Ja’afar (a.s) yana cewa: “Tir da bawan (mutumin) da handama ke jagorantar, haka nan tir da bawan da ke da nufin da ke kaskantar da shi[37]”.

Imam Aliyu bn Husain (a.s) yana cewa: “Na ga dukkan alheri ya taru….cikin kwadayin abin da ke hannayen mutane[38]”.

Haka nan daga cikin wadannan abubuwa har da kasala wanda ke sanya mutum tauye hakkokin wasu.

Ya zo cikin wasiyyar da Manzon Allah (s.a.w.a) ya yi wa Ali (a.s) cewa: “Idan ka yi kasala ba za ka sami damar ba da hakki ba[39]”.

Ya zo cikin wani hadisi na Manzon Allah (s.a.w.a) cewa: “saboda idan ya yi kasala zai tauye hakkoki[40]”.

Haka na Abul Hasan Musa (a.s) yana fadi wa dansa cewa: “Ina gargadinka kan nuna gajiya da kasala, don kuwa za su hana ka samun rabonka na duniya da lahira[41]”.

Har ila yau daga cikin wadannan shu’uri har da wauta da jahilci, dukkan wadannan biyun suna nufin mutum ya samu wani irin shu’uri cikin ransa da zai sanya shi wuce haddi da ladubba na zamantakewa cikin maganganunsa tare da sauran mutane gaba daya, ta yadda zai dinga aikata wasu abubuwa ba tare da tunani da amfani da hankali ba. Hakan na daga cikin mafi bayyanar alamun munanan dabi’u.

An ruwaito Imam Sadik (a.s) yana cewa: “Hakika kaskantar (da mutane) na daga cikin munanan dabi’u abin zargi, ya doru a kan wanda yake kasa da shi da kuma rusuna ga wanda ke sama da shi[42]”.

Kuma yana cewa: “Kada ku zamanto masu wauta, don kuwa Imamanku ba wawaye ba ne[43]”.

Daga gare shi ta hanyoyi abin dogaro yana cewa: “Mafi munin halittar Ubangiji shi ne mutumin da mutane ke tsoron harshensa[44]”.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 next