Hadiye Fushi da Juriya



Ta yadda hatta wasu malamai suna ganin shugabanci a matsayin haramtaccen lamari, saboda rashin tabbacin adalci da kuma tasirin da hakan ke samarwa na zalunci da girman kai.

Daga Mu’ammar bn Khallad, daga Abil Hasan (a.s), yayin da ya ambaci wani mutumi da cewa yana son shugabanci, sai Imam (a.s) ya ce: “………….., da ya fi cutarwa ga addinin musulmi kamar shugabanci[20]”.

Daga Abdullah bn Maskan yana cewa: Na ji Aba Abdullah (a.s) yana cewa: “Ina gargadinku da wannan shugabanni da ke jagorancin al’umma, wallahi babu….., face sai ya halaka kuma ya halakar[21]”.

Daga Imam Sadik (a.s) daga Iyayensa (a.s) daga Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: “Ku sani duk wanda ya dauki shugabancin al’umma, zai tashin Ranar Kiyama hannunsa na dauke da wuyansa, idan ya yi aiki da umarnin Allah lokacin shugabancinsa, Allah zai kunce shi, idan kuwa ya kasance azzalumi ne, za a wuce da shi zuwa wutan Jahannama, tir da wannan makoma[22]”.

b)– Fushi

Haka nan Allah Madaukakin Sarki da Ahlulbaiti (a.s) sun ja kunne dangane da fushi da kuma tasirinsa cikin alaka ta zamantakewa da kuma kamala ta shi kansa mutum, suna masu bayyana wasu hanyoyi da za a bi wajen magance wannan yanayi mai hatsarin gaske cikin rayuwar mutum tare da sauran mutane.

Saboda “Shi fushi ya kan bata imani kamar yadda ruwan inabi mai tsami ke bata zuma”, da kuma “Fushi mabudin dukkan sharri ne”, da “Mumini shi ne wanda idan ya yi fushi, fushin nasa bai kawar da shi daga gaskiya” da cewa “Wanda ya kare fushinsa daga sauran mutane, Allah Madaukakin Sarki Zai kare shi daga azabar Ranar Kiyama”, da “A duk lokacin da mutum ya yi fushi da wasu mutane alhali yana tsaye to ya zauna cikin gaggawa, saboda dattin shaidan zai kawu daga gare shi, a duk lokacin da mutum ya yi fushi da zuriyarsa, to ya kusace su ya kyautata musu, saboda idan aka kyautata wa zuriya, za su yi shiru[23]”.

Har ila yau daga cikin abubuwan da aka ruwaito kan wannan batu har da abin da Kulayni ya ruwaito daga Mu’ali bn Khanis daga Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Wani mutum ya ce wa Manzon Allah (s.a.w.a): Ya Rasulallah! Ka koyar da ni. Sai ya ce masa: Tafi ka da ka yi fushi, sai mutumin ya ce: na takaita da hakan, sai ya wuce ya tafi wajen mutanensa, ko da isarsa sai ya tarar mutanensa suna fada, sun yi sawu kowa ya dauki makami, ko da ya ga haka shi ma sai ya shirya ya dauki makaminsa, to amma sai ya tuna maganar Manzon Allah (s.a.w.a) na cewa ka da ka yi fushi, nan take sai ya yi jifa da makaminsa, ya nufi wajen daya bangaren da ke fada da mutanensa ya ce musu: Ya ku wadannan, zan biya ku cikin dukiyata dukkan abin da ya same ku na daga rauni, ko kisa ko kuma duka, sai suka ce: dukkan abin da ya wuce naku ne, mu ne muka fi dacewa da hakan sama da ku. Sai yace: sai suka sasanta tsakaninsu, fushinsu ya gushe[24]”.

c)– Hassada

Haka nan Allah Madaukakin Sarki da Ahlulbaiti (a.s) sun ja kunnen mutane kan hassada, shi ne mutum ya yi mu’amala da sauran mutane yana mai fatan kawuwar ni’imar da Allah Ya yi musu ko kuma ta tashi daga gare su ta koma wajensa.

Daga Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Lalle hassada tana cinye imani kamar yadda wuta take cin itace[25]”.

Daga gare shi (a.s) yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: Allah Madaukakin Sarki Ya fadi wa Musa (a.s): Ya dan Imrana, kada kayi hassada ga mutane kan abin da Allah Ya ba su na daga falala, kada ka sanya idanuwanka ga hakan, kada kuma zuciyarka ta koma gare shi, saboda mai hassada yana fushi ne da ni’imata, mai fada da abin da rarraba tsakanin bayina, duk wanda ya kasance haka, ba na tare da shi kuma ba ya tare da ni[26]”.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 next