Hadiye Fushi da Juriya



c)– Hakuri da Juriya

Haka nan za mu ga siffar al-hilm  (hakuri da juriya) wato mutum ya yi afuwa da rufe ido kan wasu yayin da yake cikin fushi duk kuwa da cewa yana da halin daukan mataki kan hakan. Ta yadda mutum ba ya iya zama mai ibada har sai ya kasance mai hakuri da juriya, wanda shi ne mafi daukakan mataimakin mutum a alakarsa ta zamantakewa da sauran mutane.

Daga Muhammad bn Abdullah yana cewa: na ji Imam Ridha (a.s) yana cewa: “Mutum ba ya zama ma’abucin ibada har sai ya kasance mai hakuri da juriya, ba a lissafa mutum daga cikin Bani Isra’ila a matsayin ma’abucin ibada…..shekaru goma[7]”.

Daga Abi Ja’afar (a.s) yana cewa: “(Imam) Aliyu bn Husain (a.s) ya kasance yana cewa: hakika mutumin da hakuri da juriyarsa ke riskansa yayin fushinsa na burge ni[8]”.

Abu Abdullah al-Sadik (a.s) yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: Allah ba ya taba daukaka (mutum) da jahilci, sannan kuma ba Ya taba kaskantarwa da hakuri da juriya[9]”.

d)– Sassautawa

Haka nan siffar sassautawa, wanda ita ce mu’amala da mutane cikin sauki da tausayawa sabanin gallazawa da tashin hankali, hakan na da gagarumar gudummawa a bangarori daban-daban na rayuwar dan’Adam.

Abu Abdullah (a.s) yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: sassautawa albarka ce, amfani da karfi kuma rashin sa’a ne[10]”.

Daga Abi Ja’afar (a.s) yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: Ba za a taba sanya sassauci a kan wani abu ba face ya kawata shi, kuma ba za a dage shi daga kan komai ba face sai ya munana shi[11]”.

Daga Hisham bn Ahmar, daga Abil Hasan (a.s) yana cewa: wata rana wani rikici ya shiga tsakanina da wani mutum sai ya ce min: “ka yi …..[12]”.

e)– Tawali’u

Haka nan tawali’u wanda shi ne tafarkin daukaka zuwa ga madaukakiyar daraja.

Daga Mu’awiyya bn Ammar, daga Abi Abdillah (a.s) yana cewa: Na ji shi yana cewa: “A sama akwai wasu mala’iku guda biyu da aka wakilta wa bayi, duk wanda ya yi tawali’u ga Allah za su daga shi, wanda kuwa ya yi girman kai za su yi watsi da shi[13]”.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 next