Hadiye Fushi da Juriya



Ma’anar tawali’u kamar yadda ta zo cikin cikin hadisai ita ce: “ka ba wa mutane abin da kake so a baka”, haka nan kuma “mataki-mataki ne, daga ciki akwai mutum ya san matsayinsa ya saukar da shi daidai da hakan cikin kwanciyar hankali, ba ya son ya zo ga wani mutum face tamkar yadda ake zuwa masa. Idan ya ga mummunan abu sai ya kare shi da kyakkyawa. Mai hadiye fushi, mai afuwa ga mutane, lalle Allah Na son masu kyautatawa”. Haka nan kuwa “Ya amince da wani wajen zama (taro) ba tare da wani ba, kuma ya yi sallama ga wanda ya hadu da shi, kuma ya bar jidali ku da kuwa shi ne da gaskiya, kuma kada ka so a gode maka kan takawa[14]”.

Daga Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Najashi ya aika da a kira masa Ja’afar bn Abi Talib da sahabbansa, lokacin da suka shiga wajensa sai suka same shi a zaune kan turbaya, yana sanye da wasu irin tufafi, sai Ja’afar (a.s) ya ce: sai muka ji tsoronsa yayin da muka ganshi hakan, lokacin da ya ga halin da muke ciki da canjin fuskokinmu, sai ya ce: Godiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya taimaki Muhammadu da faranta idanuwansa, ashe ba zan muku bushara ba? Sai n ace: Na’am Ya Sarki, sai ya ce: daya daga cikin mutane na dake kasarku ya zo min daga kasarku, ya ba ni labarin cewa Allah Madaukakin Sarki Ya taimaki AnnabinSa Muhammad (s.a.w.a) da kuma halaka makiyansa, ya gaya min wane da wane da wane a wani waje da ake ce ma Badar,……, shi mutum ne daga Bani Dhamra. Sai Ja’afar ya ce masa: Ya kai Sarki, me ya sa na ganka zaune kan kasa alhali kana tare da wannan ….? Sai ya ce masa: Ya Ja’afar, mum un samu cikin abin da Allah Ya saukar wa Isa (a.s) cewa daga cikin hakkin Allah a kan bayinSa da su yi maSa tawali’u a duk lokacin da wata ni’ima ta same su, don haka lokacin da Allah Ya yi min wata ni’ima da Muhammadu (s.a.w.a), sai na yi wannan tawali’un ga Allah. Lokacin da labari ya kai wajen Manzon Allah (s.a.w.a) sai ya ce wa sahabbansa: Lalle sadaka ta kan kara wa mai ita abubuwa da yawa, ku yi sadaka Allah Ya yi muku rahama, lalle tawali’u na kara wa mai shi daukaka, don haka ku yi tawali’u sai Allah Ya daga ku, haka nan afuwa na kara mai ita girma, don haka ku yi afuwa sai Allah Ya girmama ku[15]”.

Daga Mu’awiyya bn Wahab yana cewa: Na ji Aba Abdillah (a.s) yana cewa: “Ku nemi ilmi da kawata shi da hakuri da mutumci, ku yi tawali’u ga koyi ilmi daga gare shi, ku yi tawali’u ga wanda kuke bukatar ilmi daga wajensa, ka da ku kasance malamai masu girman kai don kada karyarku ta tafi da gaskiyarku[16]”.

Daga Muhammadu bn Sanan yana cewa: “Isa bn Maryama (a.s) ya gaya wa Hawariyun (sahabbansa) cewa: Ina da wata bukatar da nake so ku biya min ita, sai suka ce: Ai bukatarka ta biya Ya Ruhallah, sai ya tashi ya wanke kafafunsu, sai suka ce: ai mu ne muka cancanci haka gare ka, sai ya ce: ai mafi sani daga cikin mutane shi ne ya fi cancanta ya kasance mai musu hidima. Lalle na yi hakan ne saboda ku ma ku kasance masu tawali’u ga mutane a bayana kamar yadda nake muku tawali’u. Daga nan sai Isa (a.s) ya ce: Da tawali’u ne ake gina hikima ba da girman kai ba, haka nan a kan tudu (kasa) tsiro ke fitowa ba a kan duwatsu ba[17]”.

Daga Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) ya bude baki a yammacin alhamis a masallacin Kuba, sai ya ce: shin akwai abin sha? Sai Aws bn Khauli al-Ansari….., lokacin da ya ajiye, sai ya janye shi gefe ya ce: ai guda daga cikinsu ya wadatar, ba zan sha ba kuma ba zan haramta shi ba, sai dai kawai zan yi tawali’u wa Allah, don kuwa duk wanda ya yi tawali’u ga Allah, Zai daukaka shi, wanda kuwa ya yi girman kai Allah Zai kaskantar da shi, wanda ya yi tattali cikin rayuwarsa Allah Zai arzurta shi, wanda kuwa ya yi almubazzaranci Allah Zai hana shi arziki, wanda ke yawaita tunanin (ambaton) mutuwa Allah Zai so shi[18]”.

f)– Kyakkyawar Niyya da Manufa Ta Gari

Haka nan kyautata niyya da manufa cikin mu’amala da sauran mutane, ta yadda zai kulla alakarsa bisa wannan asasi.

Amirul Muminina (a.s) (a.s) yana cewa: “Duk wanda ya kyautata tsakaninsa da Allah, Allah Zai kyautata tsakaninsa da mutane, haka nan duk wanda ya kyautata lamurran Lahirarsa, Allah Zai kyautata masa lamurran duniyansa, duk wanda ke da mai masa wa’azi to kuwa yana da kariya daga Ubangiji[19]”.

2 - Hadiye Fushi da Siffofin Allah Wadai

A wani bangare kuma, za mu iya ganin wasu mahanga da ababen motsa rai da ke da alakar da mu’amala ta zamantakewa, da shari’a ta haramta su da kuma jan kunne kansu saboda irin abin da zasu iya haifarwa na cutarwa ga tafarkin rayuwar dan’Adam na kamala da zamantakewa.

a)– Son Shugabanci

Misali, son shugabanci da mulki da ke nuni mahanga ta mutum na son kai da sha’auce-sha’aucen zuciyarsa, Ahlulbaiti (a.s) dai sun ja kunne kan hakan musamman saboda la’akari da irin mummunar rayuwa ta fasadi da zalunci da shugabanni suke yi  a duniyar musulmi a wancan lokacin.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 next