Yin Kuka



“Ba mai zunubi wanda zai dauki zunubin wani, mutum ba shi da wani abu sai abin da ya aikata”.[19] Duk wanda ya aikata aikin alheri daidai da kwarar zarra zai samu abinsa. Kuma duk wanda ya aikata sharri dai-dai da kwarar zarra zai sami abinsa[20]. Domin a saka wa kowa abin da abin da ya yi kokari an kansa”.[21]

Sannan idan kuka ce menene dalilinku daga Sunna? sai mu ambaci wannan ruwayar kamar haka:

Manzo (s.a.w) ya tambayi wani mutum cewa: Shin wannan danka ne? sai mutumin ya bayar da amsa cewa: E.

Sai Manzo ya ce: “Bai kamata ba ya cutar da kai haka nan kai ma bai kamata ba ka cutar da shi”. Manzo (s.a.w) a cikin wannan jumla yana so ya isar da abin da Kur’ani yake cewa: Babu wanda zai cutar da wani ta hanyar zunubinsa, duk abin da mutum ya aikata yana bisakansa, wato ba zai cutar da kowa da zunubinsa ba sai kansa. Haka nan idan aikin kwarai ne zai amfanar da kansa ne.[22]

Haka nan a cikin Sahih Muslim ta hanayr Ibn Abbas, an ruwaito hadisi cewa Manzo (s.a.w) ya ce: Lallai mamaci ana yi masa azaba da kukan danginsa”. Sannan Ibn Abbas yana karawa da cewa: Lokacin da Umar ya rasu an hakaito wannan hadisi a wurin A’isha, sai ta ce: Allah ya jikan Umar, ina rantsuwa da Allah sam Manzo bai ce ba Allah zai yi wa mumini azaba sakamakon kukan wani! Amma ya ce Allah zai kara wa kafiri azaba sakamakon kukan da danginsa suke yi a kansa. Sannan wannan ayar ta wadatar da ku inda Allah yake cewa: “Babu wani mai zunubi wanda zai dauki zunubin wani”[23].

Ya dace mu yi tunatarwa a kan wani abu kamar haka cewa, Hadisin da Sahih Muslim ya ruwaito ta hanyar Hisham Bn Urwa wanda muka yi nuni da shi farkon wannan Bahasi ya inganta kuma karbabbe ne, Amma wannan hadisin da aka ruwaito daga Ibn Abbas ba ya inganta, domin kuwa kara wa kafiri azaba sakamakon kukan da danginsa suke yi bai dace da ayar Kur’ani ba.

Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com – www.hikima.org

Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)

Facebook: Haidar Center - December, 2012



 



back 1 2 3 4 5