Yin Kuka



“Ya Ibrahim ba zamu wadatar da kai komai ba a wajen Allah, Sai kwalla suka cika masa idanunsa, sai ya ce lallai Ibarahim muna tsananin bakin ciki akanka, idanuwa suna kuka zuciya tana konewa saboda bakin ciki, ba zamu fadi abin da zai fusata Ubangiji ba, ba dan mutuwa ta kasance gaskiya ba, kuma alkawari wanda ba ya canzawa ba, kuma wata hanya ce wacce dole kowa ya tafi, da bakin cikimmu na rashinka ya nunka wannan sau daruruwa.

A wannan lokacin sai Abdurrahaman Bn Auf ya ce wa manzon Allah: Ashe ba kai dakanka ka yi hani a kan kukan mutuwa ba? Sai Manzo ya bayar da amsar cewa: ba haka ba ne na yi hani ne a kan kukan da sauti guda biyu, wato kara da kuwwa a lokacin da mutum wata musiba ta same shi, sannan da yagar fuska da keta tufafi, da karar kuka wanda ake rera shi daga cikin makoshi, wanda yake wannan aikin shaidan ne, ko kuwa ayi shi da yanayin waka ta haram. Amma wannan kukan nawa ya samo asali daga tausai da kauna, Sannan duk wanda bai tausaya ba, ba za a tausaya masa ba[3].

Wannan misali na sama ba shi kadaiba ne misali wanda Manzo ya yi kuka a kan rasa wani nasa. Manzo a lokacin dansa Tahir ya rasu ya yi kuka kuma yana cewa: “Idanuwa suna kuka zuciya tana konewa saboda bakin ciki amma ba zamu yi sabon Allah ba”[4].

Allama amini a cikin littafinsa mai dimbin daraja “Al-gadir” ya kawo a wurare da dama inda Manzo ya yi kuka sakakamon rasa wani nasa da ya yi. Misalan da zamu kawo a kasa suna daga cikin misalan da Allama Amini ya kawo:

1-Lokacin da Hamza Allah ya jikansa ya yi shahada a yakin Uhd, Safiyya diyar Abdul Mutallib ta tafi tana neman Manzo lokacin da ta ga Manzo, sai Manzo ya shiga tsakaninta da Ansar ya ce: ku kyale ta da abin da ya dame ta, Safiyya ta zauna kusa da gawar Hamzata yi kuka. Duk lokacin da muryar kukanta ta yi sama, sai Manzo shi ma kukansa ya yi sama, idan ta yi kuka a hankali sai Manzo shi ma ya yi a hankali. Haka nan Fadima (a.s) ‘yar Manzo ta kasance tana kuka Manzo shi ma yana kuka tare da ita, yana cewa: Babu wanda musiba zata taba shafa kamar ki.[5]

2- Bayan yakin Uhd Manzo ya dawo Madina, sai ya samu labarin cewa matan Madina suna yin kuka a kan danginsu da suka yi shahada a Uhd, sai Manzo ya ce: Shi Hamza bashi da mai yi masa kuka? Lokacin da Ansar suka ji wannan kalami na Manzo, sai suka cewa matansu: Duk wanda yake so ya yi kuka a kan shahidinsa ya fara yin kuka a kan Hamza baffan Manzo. (Kamar yadda mai littafin “Zawayid yake cewa har yanzu wannan abin haka yake duk lokacin da wani zai yi wa mamacinsa kuka sai ya fara da yi wa Hamzakuka”.[6]

3-Lokacin da labarin shahadar Ja’afar, Zaid Bn Harisa da Abdullahi Bn Rawaha ya iso wa manzon Allah, kwalla sun zubo daga idanun Manzo.[7]

Lokacin da Manzo ya je ziyarar Mahaifiyarsa ya yi kuka kwarai da gaske, sakamakon wannan kukan nasa ne wadanda suke tare da shi suka fashe da kuka.[8]

4-Lokacin da Usman Bn maz’un ya rasu, wanda yake daya daga cikin sahabban Manzo (s.a.w) Manzo ya sumbaci gawarsa kuma ya yi kuka, ta yadda kwallansa suka gudana bisa kuncinsa.[9]

5-Lokacin da wani daga cikin ‘ya’yan ‘yar Manzo ya rasu ya yi kuka, sai Ubada Bn Samit ya tambaye shi me ya sa yake kuka? Sai Manzo ya ba shi amsa da cewa: Kuka rahama ce wacce Allah ya bai wa ‘yan Adam, Allah madaukai zai ji kan bayinsa wadanda suke da tausayi.[10]



back 1 2 3 4 5 next