Yin Kuka



6-Sayyida Zahara (a.s) bayan rasuwar Manzo ta yi kuka kwarai da gaske, tana cewa: Ya kai babana! Ka kusanci ubangijnka, kuma ka karba kiransa, ya baba masoyina, muna isar da labarin rasuwarka zuwa ga Jibrilu, kuma aljannar Firdausi ita ce makomarka[11].

7-‘Yar Manzo Fadima (a.s) ta tsaya a kan kabarin babanta, ta debi kasar kabarin a cikin hannunta, ta dora a kan idanunta tana kuka tana cewa a cikin waka:

“Me zai faru ga mutum idan ya shaki kasar kabarin Ahmad,

Don bai shaki turare mai tsada ba a duk tsawon rayuwarsa.

Musiba ta sauka a kaina wacce idan da

Ta sauka ne a kan yini zai koma dare.

A yakin Uhud gwaggon Jabir Bn Abdullah ta kasance tana kuka a kan dan’uwanta Abdullah Bn Umar da aka kashe.

Sai Jabir ya ce ina kuka mutane suna hana ni yin kuka, amma Manzo bai hane ni da yin kuka ba. Sai Manzo ya ce: “Ka yi kuka a wajen zaman makokinsa domin kuwa ka rasa masoyi, kuma kada ka yi kuka domin kuwa, ina rantsuwa da Allah zuwa lokacin da aka rufe shi a cikin kabari mala’iku sun yi masa inuwa da fika-fikansu”. [12]

Amma dangane da ruwayar da ta zo daga Umar da dansa Abdullah Bn Umar cewa Manzo ya ce: “Lallai ana azabtar da mamaci a kan kukan danginsa”.

A ra’ayimmu zahirin wannan hadisi ya yi karo da yadda tarihin rayuwar khalifa na biyu, wannan kuwa ya hada da:



back 1 2 3 4 5 next