Yin Kuka



1-Lokacin da labarin mutuwar nu’uman Bn mukarrin ya iso wa Umar, lokacin da umar ya fito daga gida ya hau kan mimbari ya isar da wannan labari ga mutane, a wannan lokaci sai ya dora hannunsa a bisa kai ya yi kuka.[13]

2-Lokacin da Khalid Bn Walid ya rasu, Umar ya yi kuka a wajen zaman makokinsa, lokacin da labari ya iso masa cewa wasu sun hana mata su yi kuka sai ya ce: Idan har kukan ba suna daga murya suna kakari ba ne, babu wani laifi a kansa. [14]

3-Lokacin da dan’uwan Umar ya rasu, sai wani abokinsa daga kabilar bani Ka’ab ya zo Madina, da Umar ya ga wannan abokin dan’uwansa, sai kwalla suka kwararo daga idanunsa ya ce: Zuwanka ya tuna mini Zaid![15]

Wannan kuka na khalifa Umar a wurare masu yawa, zai fahimtar da mu cewa ma’anar wannan hadisi koda kuwa danganensa ya inganta to yana nufin wani abu daban ne. Sannan bugu da kari idan har muka amince da zahirin wannan hadisi, to zai yi karo ne da ayar Kur’ani. Domin kuwa aya tana cewa: “Babu wani wanda zai dauki zunubin wani”.[16] Don haka idan aka azabtar da wani mamaci sakamakon kukan da danginsa suka yi, me zai kasance ma’anar wannan kenan?

 

Bincike Dangane Da Ma’anar Hadisin

Abubuwan da muka fada a baya zasu fahimtar da mu cewa idan har danganen wannan hadisi ya inganta, to ma’anarsa zata zama sabanin zahirin abin da yake nunawa, domin kuwa hadisin yana cewa ne “ana azabatar da mamaci sakamakon kukan da danginsa suke yi”. Saboda haka muna ganin cewa wannan hadisi akwai wasu alamu da suke nuni da wani abu, yayin da aka ruwaito shi, ba a ruwaito da wadannan alamomi ba, sakamakon haka ne wasu suka fahimci cewa kukan mutuwa ya haramta, alhalin an rabkana daga ma’anarsa ta hakika.

A cikin Sahih Muslim, an ruwaito daga Hisham Bn Urwa shi kuma daga babansa cewa, an ruwaito daga A’isha ta hanyar Ibn Umar cewa: Ana yi wa mamaci azaba sakamakon kukan da danginsa suke yi”. Sai A’isha ta ce: Allah ya rahamshe da baban Abdurrahaman, domin ya ji wani abu amma bai iya rike shi ba. Hakikanin al’amarin shi ne wata rana an wuce ta wajen Manzo da gawar wani bayahude, sai mutanensa suna yi masa kuka, sai Manzo ya ce: “Kuna yi masa kuka alhali shi yana cikin azaba”.[17]

Abu Dawud a cikin littafin sunan dinsa, ya ruwaito ta hanyar Urwa shi kuma daga Ibn Umar yana cewa: Wannan jumla da take cewa “Ana azabtar da mamaci sakamakon kukan danginsa”. Daga manzon Allah take. Lokacin da wannan labari ya kai wa A’isha sai ta ce: Lokacin da Manzo zai gitta kabarin wani bayahude sai ya ce: Mai wannan kabarin yana cikin azaba, alhalin danginsa suna yi masa kuka. “Sai ya karanta wannan aya: “Babu wani mai zunubi da zai dauki zunubin wani”. [18]

Imam Shafi’i yana cewa: Abin da A’isha ta ruwaito dangane da wannan magana tare da amfani da abin da Kur’ani da Sunna suke koyarwa ya fi kama da maganar Manzo a kan abin da Ibn Umar yake fada. Idan kuwa kuka ce menene dalilinku a kan haka daga Kur’ani to zamu kawo wannan ayar kamar haka:



back 1 2 3 4 5 next