Kamun kafa Da Annabawa Da Waliyan Allah 3



A nan yana nuna ya yi kamun kafa ne da shi kansa manzon sakamakon girmansa a wajen Allah yake neman biyan bukatunsa.

2-jumlar “Muhammad annabin rahama”

Wannan jumla tana nunawa a fili cewa Manzo wanda yake rahamar Ubangiji ce a bayyane, shi ya sanya yake kamun kafa da wannan rahama da Ubangiji zuwa ga Allah.

Abin mamaki a nan shi ne irin wannan al’amari ya sake faruwa a zamanin Usman. Sannan matsalar mutumin da yake neman biyan bukata a wannan lokaci ta warware ne ta hanyar wannan addu’a, amma akwai bambanci kadan cewa wanda ya koyar da wannan addu’a a lokaci na farko shi ne Manzo da kansa, amma alokacin na biyu Usman Bn Hanif ne, a nan zamu kawo cikakken abin da ya faru daga mu’ujamul kabir na Dabarani kamar haka:

Wani mutum a zamanin hukumar Usman ya je wajen Usman domin wata bukata tasa amma bai samu biyan bukata ba, wata rana wannan mutum sai ya hadu da Usman Bn Hanif kuma ya gaya masa abin da yake damunsa, sai ya ce masa: ka je ka yi alwala ka yi salla raka biyu, sannan ka ce:

“Ya Allah ina rokonka kuma ina fuskantarka da manzommu Muhammad annabin rahama, ya Muhammad ina kamun kafa da kai zuwa wajen ubangijinka don a biya mini bukatata”.

Sai ya aikata wannan aiki, sannan ya tafi wajen Khalifa sai kuwa ya biya masa bukatarsa, sai ya sake haduwa da Usman Bn Hanif, ya tambaye shi danganen wannan addu’a, sai ya ce masa wata rana mun kasance a wajen Manzo (s.a.w) sai wani mutum mai ciwon ido ya zo wajen Manzo ya nemi ya yi masa addu’a, sai Manzo ya koyar da shi abin da na koyar da kai. [11]

3-Jumlar “Ya Muhammad ina fuskantar Ubangiji da kai”.

Wannan lafazi na “da kai”yan nuna kamun kafa ne da shi kansa Manzo din, saboda haka duk da cewa ya roki Manzo addu’a, amma ba shi ne matsayin shedarmu ba a nan. Amma a cikin abin da Manzo ya koyar da shi akwai shi kansa Manzo wanda yake rahamar Allah ne a cikin halitta, kuma shi ne silar biyan bukatar wannan makaho. Sannan jumlar “Ka ba shi lafiya don girmana” ita ma tana nuni ne ga sakamakon girman za a wajen Allah, zai samu biyan bukatarsa.

Wata kila a fahimci cewa wannan jumla ta sama tana nufin cewa; Ya Allah! Ka karbi addu’arsa da na yi masa, amma zahirin wannan hadisi ba ya nuna cewa Manzo ya yi wa wannan makaho addu’a, domin kuwa ya koyar da shi ne addu’ar kamar yadda muka yi bayani a sama. Ballantana Manzo ya bukaci Allah ya amsa addua’r da ya yi masa don girmansa a wajen Allh. Idan kuwa da Manzo ya yi wa wannan makaho addu’a bayan addu’ar da ya kowar da shi, to tabbas da wannan babban sahabi ya ruwaito wannan addu’a ta Manzo.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 next