Kamun kafa Da Annabawa Da Waliyan Allah 3



Kamun kafa Da Annabawa Da Waliyan Allah 3

 

Mawallafi: Ayatullahi Ja’afar Subhani

Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani

Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id

Ibn Taimiyya Da Mabiyansa

Ibn Taimiyya da mabiyansa suna cewa: Neman addu'a daga Manzo ya kebanta ne da zamanin rayuwarsa ne a duniya kawai, don haka wannan ba ya halatta bayan wafatin Manzo! Haka ne zai yiwu mutum ya ziyarci Manzo, sannan ya yi addu’a a gefen kabarinsa sannan ya nemi abin da yake so a wajen Allah.[1]

Dangane da amsar wannan magana kuwa zamu yi fadakarwa a kan cewa, dole ne a fahimci matsayi da darajar Manzo a wajen Allah, wato matsayin da zai sanya al’ummar musulmi masu zunubi su zo wajensa domin ya nema musu gafarar Ubangiji ta yadda addu’arsa karbabba ce.

Shin wannan matsayi da daraja ta Manzo ya samu asali ne daga jikinsa ko kuwa wani abu wanda ya shafi rayuwar duniya, ta yadda sakamakon wafatinsa zai kawo karshe, ko kuwa wannan matsayin sakamakon tsarki da daukakar ruhinsa ne?

Ra’ayi na farko kuwa ya saba wa hankali da shari’a, domin kuwa kamar yadda muka yi bayani a cikin bahsin rayuwar barzahu mun ga yadda ya kasance cewa; hakikanin mutum ruhinsa ne ba jikinsa ba. Sannan mun ga cewa ruhin mutum bayan rasuwarsa zai ci gaba da rayuwa a rayuwar barzahu, wato mutuwa ba yana nufin karshen rayuwa ba ne, ci gaba ne da rayuwa a wata duniyar ta daban. Don haka matsayi da daukakar Manzo ta samo asali ne daga girma da daukaka na ruhinsa, don haka bayan wafatinsa wannan matsayi yananan kamar yadda yake lokacin da yake a raye.



1 2 3 4 5 6 7 8 9 next