Kamun kafa Da Annabawa Da Waliyan Allah 3



Ya Allah ina rokonka ina fuskantarka da manzonka Muhammad wanda yake annabin rahama ne ina kamunka kafa da shi a wurinka! Ya manzon Allah ina Kamun kafa da kai a wajen Allah domin ya biya mini bukatata. Sai Manzo ya ce: Ya Ubangiji ka biya masa bukatarsa domin ni.

Ibn Hanif yana cewa: Mun kasance a wajen Manzo ba tare da tsawon lokaci ba sai wannan mutum ya shigo a wajenmu kamar bai taba samun matsalar ido ba. Kafa hujja da wannan hadisi kuwa ya samo asali ne ta hanyar kasantuwar ingancin dangane da kuma ma’anarsa wacce take a fili.

Amma ta bangaren dangane da wannan hadisi kuwa Tirmizi yana cewa: wannan hadisi ne mai kyau kuma ingantacce. Ibn maja shi ma wanda ya ruwaito wannan hadisi yana cewa: wannan hadisi ne ingantacce. Sannan cikin sa’a shi ma Ibn Taimiyya ya tafi a kan ingancin wannan hadisi.[9] Rufa’i wanda yake daya daga cikin marubutan wahabiyawa kuma na wannan zamani yana cewa: Babu shakka a kan kasantuwar ingancin wannan hadisi kuma mashahuri ne.[10]

Saboda haka dangane da sanad ko danganen wannan hadisi babu sauran wani kace-nace. Saboda haka a nan abin da ya yi saura shi ne muyi bincike dangane da ma’anarsa a kan halascin wannan nau’i na kamun kafa.

Domin kuwa bayyana wannan ma’ana zamu tunatar da wasu abubuwa guda biyu kamar haka:

1-Menene makaho ya nema a wajen Manzo?

2-Domin ya samu biyan bukata wane irin Tawassuli ko kamun kafa da Manzo ya koyar da shi? !

Cakuda wadannan abubuwa guda biyu zai sanya a kasa gane gaskiyar al’amarin, babu shakka wannan makaho ya roki addu’a daga Manzo, wato ya yi kamun kafa da addu’ar Manzo, a nan babu sabani a kan hakan.

Magana kuwa tana nan a cikin abin da Manzo ya koyar da wannan makaho, a cikin wannan addu’a da Manzo ya koyar da shi ya nuna masa ne ta yadda zai yi kamun kafa da shi kansa manzon, wato ya sanya Manzo tsakiya a tsakaninsa da Ubangiji, ta yadda sakamakon haka Allah ya biya masa bukatunsa. Sheda kuwa a kan hakan shi ne jumlolin da suka zo a cikin hadisin wadanda suke nuni da hakan. su ne kuwa kamar haka:

1- “Ya Allah ina rokonka ina fuskantarka da annabinka” wato ina rokonka da annabinka kuma ina fuskantarka da annabinka. Wace jumla ce ta fi wannan bayyana a kan cewa mai addu’a yana hada Allah ne da manzonsa wajen neman biyan bukatarsa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 next