Kamun kafa Da Annabawa Da Waliyan Allah 3



Wadanda suke da wannan tunani suna ganin tsakaninmu da wadanda suka rasu akwai wani abu wanda ya kare tsakanimmu, wanda Kur’ani yake ambata da barzahu. “A bayansu a kwai barzahu, har zuwa ranar tashin kiyama”.[3] Don haka kirammu ba zai isa zuwa gare su ba.

Amsa: Barzakh a harshen larabci ba tana nufin shamaki ko hijabi ba, wato ana nufin shamaki wanda yake hana su dawowa zuwa rayuwar wannan duniya, ba wai abin da zai hana su alaka da wadanda suke a raye ba. tare da kula da ayar da take da alaka da barzahu muna iya fahimtar wannan al’amari kamar yadda Kur’ani yake cewa:

“Zuwa lokacin da mutuwa zata zo wa daya daga cikinsu, zai ce: Ubangiji ka mai da ni zuwa duniya, domin kuwa zanyi aiki mai kyau a cikin abin ya ragu gare ni, sam ba haka ba ne kawai magana ce wacce mai yin ta yake fada”.[4]

Tare da kula da abin da mamaci yake fada shi ne Kur’ani yake ba shi amsa da cewa: “A bayansu akwai abin da ya kare su ta yadda ba zasu koma ba har zuwa ranar kiyama”.[5] Saboda haka wannan shamaki na hana dawowa a duniya ne, ba wanda zai hana wadanda suka rasu ba su yi alaka da wadanda suke a raye.

Tambaya ta hudu: Shin Manzo yana jin maganarmu?

Kur’ani yana kamanta yadda mushirikai suke da matattu, manufarsa kuwa da wannan shi ne, kamar yadda matacce ba ya jin magana, masu shirka suma haka suke, a kan haka ne yake cewa: “Lallai kai ba ka iya jiyar da matattu”[6] “sannan ba ka iya jiyar da wadanda suke cikin kabari”[7]Dangane da kamanta mushirikai da matattu dangane da rashin jin magana, muna iya cewa wani abu ne wanda babu shakku a cikinsa cewa an kamanta mushirikai da matattu.

Amsa: Babu shakka a cikin kowace kamantawa ko misaltawa a kwai wata fuska da abu guda biyu a kan kamanta su, misali lokacin da za a ce Ali kamar zaki yake, tabbas a nan an dauki fuskar jarunta ne aka siffanta Ali da zaki domin kuwa duka guda biyun suna da wannan siffa. Saboda haka a nan zamu ga menene fuskar da ta sanya a kamanta matacce da mushiriki?

Tabbas babu yadda za a ce ta fuskar cewa sam ba su ji ko kadan, domin kuwa idan muka dauki hakan cewa mamaci ba ya ji, to shi ma mushiriki zai rasa wannan halitta ta ji ke nan, ga shi kuwa mushiriki yana jin maganar Manzo da ma ta sauran al’umma.

Saboda haka wannan kama da ta sanya aka kamanta su da wani abu daban, wannan kuwa shi ne rashin sauraren magana mai amfani. Wato kamar yada kiran wanda ya mutu zuwa ga aiki mai kyau ba shi da amfani, domin kuwa lokacin aikin ya riga ya gabata, haka nan kiran mushrikai zuwa ga aiki mai kyau ba shi da wani amfani, domin kuwa sam ba su da niyyar amsa wannan kira, tare da lura da ayoyin da suke magana a kan rayuwar barzahu zamu iya fahimtar wannan hakika.

Saboda haka magana guda a nan ita ce, kiran mushrikai zuwa ga imani kamar kiran wadanda suka mutu ne zuwa ga aiki mai kyau. Don haka kiran wadannan gungu guda biyu (Mushrikai da matattu) sam ba zai samu wata riba ba. Mushiriki yana ji amma ba shi niyyar karbar gaskiya, mamaci shi ma yana ji amma lokacin aiki ya riga ya wuce yanzu lokacin sakayya ne ga abin da mutum ya aikata ne.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 next