Kamun kafa Da Annabawa Da Waliyan Allah 2



4- Gazali (ya rasu 505) Dangane da falalar ziyarar Madina da yadda ake ziyarar Manzo ya ruwaito a bayyane yana cewa: Bayan mutum ya gama sallama ga Manzo, sai ya dubi kabarin Manzo yana tsaye, sannan ya yi godiya ga Allah da yabonsa, sai ya aika gaisuwa mai yawa zuwa ga Manzo, sannan ya karanta wannna ayar da take cewa: Da wadanda suka zalunci kawunansu sun zo, sannan ya ce ya Allah mun ji kiran ka kuma mun amsa umurninka, sannan mun yi kamun kafa da manzonka muna neman cetonka daga zunubbammu, lallai zunubbai masu nauyi sun yi mana yawa…”

5- Sheikh Hasan Bn Ammar sharanbalani a cikin littafinsa “Murakil falah” yana ruwaito ziyarar Manzo kamar haka:

“Amincin Allah ya tabbata gareka ya kai shugabana ya manzon Allah, Amincin Allah ya tabbata a gareka ya annabin Allah! Lallai kurakurai sun karya mana kashin baya, sannan nauyin zunubban ya yi mana yawa a kan kafadummu. Kai ne mai ceto kuma wanda ake karbar cetonsa. Allah madaukaki ya yi maka alkawarin ceto da matsayi mai girma kuma abin yabo a wurinsa, sannan yana cewa: “Duk lokacin da suka zalunci kawunansu sannan suka zo wajenka suna masu neman gafarar Allah sannan Manzo ya nema musu gafara a wajen Allah, zamu samu Allah mai karbar tuba kuma mai jin kai.

Mun kasance mun zalunci kawunammu ga mu mun zo wajenka sannan muna neman gafara dangane da zunubbammu, ka nema mana gafara a wajen Allah”.

6- Sayyid Ibn Dawus (ya rasu 664) ya ruwaito yadda ake ziyarar Manzo daga Imam Sadik (a.s) ga abin da yake cewa: Ya Ubangiji kai ne ka ce wa manzonka duk lokacin da suka zalunci kawunansu kuma suka zo wajenka suna neman gafarar Allah, sannan Manzo yanema musu gafara, zasu samu Allah yana mai karbar tuba kuma mai jin kai”[16]

Ya Ubangiji ban kasance ina rayuwa a zamanin Manzo ba, amma yanzu na zo ziyararsa, kuma ina mai tuba daga munanan ayyukana, kuma ina neman gafara daga zunubbaina kuma ina mai ikrari a kan aikata su”.

Mun kawo wasu daga cikin misalai dangane da yadda ake ziyarar Manzo, sannan mun ga yadda suka hadu a kan karanta wannan aya ga mai ziyara. A hakikanin gaskiya wannan aya wani nauyi ne aka aza wa mai ziyara aka kuma aza wa Manzo:

Amma nauyin da aka aza wa mai ziyara shi ne, mutum ya je wajen Manzo ya nemi gafarar zubbansa, sannan nauyin da ya hau kan Manzo shi ne ya neman wa mai ziyara gafara a wajen Allah.

Dukkan wadannan ladubban ziyara suna nuna mana yadda mai ziyara yake neman ceto daga Manzo a yayin da ba shi duniya, babu bambanci da lokacin da yake raye ta yadda mutum zai yi kamun kafa da shi.

Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com – www.hikima.org – www.haidarcip.org



back 1 2 3 4 5 6 7 8 next