Kamun kafa Da Annabawa Da Waliyan Allah 2



Sai na ukkunsu ya ce: Wata rana na kawo wa babana da mamana kwanon madara sai na tarar da su duk suna barci. Sai na yi tunani a cikin raina cewa idan na ajiye musu wannan madara a kasa na tafi gida mai yiwuwa kafin su tashi kuda ko sauro ya fada musu a cikin wannan madara, sannan kuma ba ni so in tayar da su daga barci. saboda haka sai na yi tsaye da wannan madara har suka ta shi daga barci sannan suka sha wannan madara. A wannan lokaci sai kofar kogo ta bude dukkanta suka fita daga wannan hali da suka shiga. [6]

Wannan kissa kuwa masu hadisi daga bangare guda biyu Sunna da Shi’a sun kawo ta duk da cewa akwai sabani a wasu abubuwa.

4-Kamun kafa Da Adu’­ar Manzo (s.a.w)

Manzo (s.a.w) mutum ne wanda yake ya fi kowa girma da daukaka a cikin dukkan halittar da Allah ya yi, Ayoyin Kur’ani sun yi nuni da haka a wurare da dama, saboda haka ba zai yiwu ba mu kawo dukkansu a wannan wuri.

Dangane da darajar Manzo ya wadatar da mu a kan cewa yana matsayin mai kare al’umma daga azabar Allah, Allah yana bayyanarwa a cikin Kur’ani cewa, matukar Manzo yana a cikin al’umma to Allah ba zai kama wannan al’ummar ba da azaba ba, kamar yadda yake cewa: Allah bai kasance zai azabtar da su ba matukar kanacikinsu, sannan Allah ba zai azabtar da sub a matukar suna neman gafara”. [7]

Sannan ya wadatar da mu a kan girman Manzo inda Allah madaukaki ya sanya sunan Manzo a gefen sunansa, sannan ya sanya biyayya ga Manzo tare da biyayya ga Allah, a kan haka Allah yana cewe: “Duk wanda ya bi Allah ya bi Manzo, lallai ya samu babban rabo”. [8]

Wadannan ayoyi da masu kama da su suna bayyanar da dajara da karama ta Manzo (s.a.w) matsayi da darajar da babu wani a cikin halitta wanda yake da shi, sakamakon wannan matsayin da daukaka da Manzo yake da shi a wajen Allah duk abin da yaroka za a biya masa bukatarsa. Don haka ne aka bai wa masu laifuka da zunubbai umurnin cewa, su nemi Manzo daya nema musu gafara a wajen Allah, inda Allah madaukaki yake cewa: “Da wadanda suka zalunci kawunansu zasu zo maka suna masu neman gafara a wajen Allah, kuma Manzo ya nema musu gafara, da sun samu Allah yana mai gafara kuma mai karbar tuba”.[9]

Sannan zamu iya fahimta daga wasu ayoyi cewa, sakamakon matsayi da daukaka manzanni sun kasance ana iya kamun kafa da su a wajen Allah kamar yadda zamu gani dangane da ‘ya’yan annabi Yakub (a.s) lokacin da kuskuransu ya bayyana a fili, sai suka cewa mahaifinsu: “Ya babanmu ka nema mana gafara lallai mun kasance masu kuskure. Sai ya ce musu zan nema muku gafara a wajen ubangijina, kuma lallai shi mai gafara ne mai rahama”.[10]

Dangane da halascin wannan nau’i na kamun kafa babu wani shakku a cikinsa, domin kuwa babu sabani a kan haka. Abin da yake da muhimmanci a nan shi ne, sanin dalilin da ya sa nya ake karbar addu’ar annabawa.

Babu shakka tushen abin da ya sanya ake karbar addu’ar annabi ya samo asali ne daga tsarkin ruhinsa, sannan da kusancinsa ga Allah madaukaki. Don haka sakamakon wannan girma da daukaka ne na ruhi ya sanya Allah yake karbar addu’arsu.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 next