Kamun kafa Da Annabawa Da Waliyan Allah 2



Babu shakka addu’ar da ta taso daga ruhi mai tsarki wanda yake cike da soyayyar Ubangiji, ba tare da wani bata lokaci ba zata samu karbuwa a wajen Allah madaukaki.

Idan har akwai wata magana a kan halascin wannan kamun kafa kuwa, zai kasance ne dangane da kamun kafa da annabawa yayin da suka rasu wato lokacin da ba su raye a duniya. Tare da kula da abin da muka fada a wajen ziyarar kabari, mun yi bayani kan cewa babu wani bambanci tsakanin lokacin da annabawa suke a raye da lokacin da ba su raye a duniya, domin kuwa Manzo a cikin wadannan hali guda biyu yana iya nema wa mutum gafara a wajen Allah. Zamu yi cikakken bayani a kan wannan a cikin nau’in kamun kafa na shida insha Allah.

5-Kamun kafa Da Addu’ar Dan’uwa Mumini

Kur’ani yana bayyanar da cewa mala’iku suna yi wa masu imani addu’a, kamar haka:

“Wadanda suke daukar al’arshi da na gefensa, suna tasbihi da godiyar ubangijinsu, kuma suna masu imani da shi, sannan suna neman gafara ga wadanda suka yi imani”[11].

Wannan ba yana nuna cewa ba mala’iku ne kawai suke yi wa masu imani addu’a. Domin kuwa Kur’ani a fifli yana bayar da labarin yadda muminai suke wa junansu addu’ga abin da Kur’ani yake cewa: “Wadanda suka zo a bayansu, suna cewa, ya ubangijinmu! Ka yi mana gafara da ‘yan’uwammu wadanda suka riga mu da imani, ya Allah kada ka sanya jin zafin a cikin zukatanmu dangane da wadanda suka yi imani, ya Allah kai ne mai rangwame mai rahama”. [12]

A cikin ayoyin da muka ambata a sama zamu iya fahimtar cewa, addu’ar mala’iku masu daukar al’arshi da kuma addu’ar muminai a kan ‘yan’uwansu ta cancanci karbuwa. Saboda haka wannan aya tana nuna mana cewa mutum yana iya neman addu’a daga mala’ku da kuma sauran ‘yan’uwansa masu imani.

Dangane da karbar adduar mumini kuwa, ya wadatar da mu inda Manzo (s.a.w) yake neman muminai su yi masa addu’a, inda yake cewa: Ku nema mini tsani a wajen Allah domin kuwa matsayi ne a cikin aljanna, babu kuwa wanda zai samu wannan matsayin sai wasu da suka cancanta daga cikin bayinsa, ina fata in zama nine, don haka duk wanda ya nemi kamun kafa da ni, cetona ya halasta gare shi”. Kasantuwar wannan kamun kafar ya karbu a wajen dukkan musulmi ba tare da wani sabani ba, muna iya wadatuwa da wannan.

6-Kamun kafa Da Addu’ar Manzo Bayan Rasuwarsa

Bahsin da ya gabata ya tabbatar mana yadda kofofin rahama suka kasance a bude ga masu laifuka, ta yadda zasu iya kamun kafa da Manzo kamar yadda aya take nuni da hakan (da wadanda suka zalunci kawunansu sun…) wato suka nemi Manzo da ya neman musu gafara a wajen Allah. Sakamakon haka ne Kur’ani yake zargin munafukai domin kasantuwarsu sun rasa wannan falalar mai dimbin yawa. Ga abin da yake cewa: “Duk lokacin da aka ce musu, ku tafi zuwa Manzo domin ya nema muku gafara sai su kawar da kansu”.[13]



back 1 2 3 4 5 6 7 8 next