Kamun kafa Da Annabawa Da Waliyan Allah 2



A-Karbar wannan aiki daga dukkan su biyun.

B-Allah ya sanya su masu biyayya a gare shi.

C-Koyar da su aikin hajji.

D-Karbar tubarsu da sanya su a cikin rahama.

2-A cikin wata ayar ga abin da ya zo: “Muminai wadanda suke cewa: Ya Allah lallai mun yi imani ka yi mana gafara a kan zunubbammu, sannan ka tseratar da mu daga azabar wuta”.[5]

A cikin wannan aya sun roki Allah da cewa ya gafarta musu zunubbansu sakamakon ayyukan kyawawa inda suke cewa “lallai mun yi imani da kai”.

Kamar yadda muka yi bayani a baya, ayoyin Kur’ani sun yi nuni da halascin kamun kafa da ayyuka na gari duk da cewa ba a bayyane ba ne. Amma a cikin ruwayoyi an yi bayanin hakan a fili. Sannan masu ruwaito hadisi daga bangarori guda biyu, sun ruwaito cewa wasu muminai guda uku sun kasance a cikin daji, sai ruwan sama ya taso, sai suka shiga cikin wani kogo domin su buya. Amma cikin rashin sa’a sakamakon wannan ruwa da iska sai wani bangaren dutse ya gangaro daga sama ya rufe kofar wannan kogo, a wannan lokaci sai daya daga cikinsu ya ce: Fadin gaskiya ce kawai abin da zai fitar da mu daga cikin wannan dutse, don haka ku zo duk wanda ya yi wani kyakkyawan aiki ya fada, sai mu roki Allah sakamakon albarkacin wannan aiki ya tseratar da mu. Dukkansu ukun suka fadi wani aiki wanda suka yi saboda Allah, kamun kafar da suka yi da wadannan ayyuka na su, cikin ikon Allah sai wannan dutse ya bude suka fita daga wannan hali da suka shiga.

Malamin Hadisi Baraki (ya rasu shekra ta 274) bayan ya ambaci wannan labari sai ya ce: Daya daga cikinsu cewa ya yi, ya kasance na baiwa wata mace kudi domin mu aikata wani aiki wanda bai dace ba, sannan kuma ita ma ta shirya a kan hakan, amma sai na tuna cewa akwai azabar lahira ga masu yin hakan, sai na kaurace wa wannan aiki, a wannan lokaci sai kofar ta dan bude kadan.

Sai daya kuma daga cikinsu shi ma ya ce:

Na ksance na tara wasu mutane domin su yi mini aikin kwadago, sannan zan ba kowane daya daga cikinsu rabin darhami matsayin ladar aikinsu. Bayan sun gama wannan aiki sai wani daga cikinsu ya nemi in ba shi darhami guda, wato a matsayin shi ya yi aikin mutum biyu ne, amma sai ban amince da abin da ya fada ba, sai bai amshi komai ba ya fita, (sai na kasance na yi amfani da kudin na wadanda suke a hannuna) na yi noma sannan kuma na samu amfani mai yawa. lokacin da ya ji wannan labari sai ya zo a wajena, sai ba shi darhami dubu goma, ya Allah na yi wannan aiki ne domin neman yardarka. a wannan lokaci sai kofar kogo ta dan kara budewa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 next