Kamun kafa Da Annabawa Da Waliyan Allah 2



Kamun kafa Da Annabawa Da Waliyan Allah 2

 

Mawallafi: Ayatullahi Ja’afar Subhani

Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani

Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id

Yanzu kuma lokaci ya yi inda zamu bayyanar da kashe-kashen neman tsani ko kamun kafa da wata ma’anar, sannan mu yi bayanin hukuncin kowane ta yadda ya dace da Kur’ani da Sunna ko kuma sabanin hakan.

Kamun kafa yana da kashe-kashe kamar yadda zamu ambata a kasa kamar haka:

1-Kamun kafa Da Sunaye Da Siffofin Allah

Daya daga cikin rabe-raben kamun kafa ko neman tsani zuwa ga Allah shi ne neman kusanci zuwa ga Allah ta hanyar kiran sunaye da siffofinsa. Wannan nau’i kuwa na kamun kafa ko tawassuli ya zo da yawa a cikin ruwayoyin Ahlul baiti (a.s), amma a nan kawai zamu wadatu da hadisai guda biyu da suke nuni a kan haka:

Tirmizi a cikin Sunan dinsa ya ruwaito daga Buraida shi kuma daga Manzo (s.a.w) cewa yaji wani mutum yana cewa: Ya Allah ina rokon da kasantuwar na sheda cewa babu abin bauta da gaskiya sai kai, sannan kai kadai ne kuma mai biyan bukata, sannan ba a haife ka ba kuma ba ka haifa ba, sannan babu wani wanda ya yi daidai da kai.



1 2 3 4 5 6 7 8 next