Girmama Kaburbura Masu Tsarki



 Kowa ya san cewa an rufe Manzo (s.a.w), a cikin gidansa, wato a wurin da ya kasance yana ambaton Allah da yabonsa. Saboda haka tare da bin hukuncin wannan aya gidan Manzo ya cancanci girmamawa da daukaka matsayinsa, sannan a kiyaye shi daga kowane irin rushewa da lalacewa. Sannan kuma a kaurace wa sanya masa duk wani nau’i na kazanta, kai da yawa daga bangarorin Madina kaburburan manyan bayin Allah ne. Kamar yadda ya zo a cikin ingantattun ruwayoyi sayyida Fadima (a.s) ita an rufe ta ne a cikin gidanta[15]

 Haka nan Imam Hadi da Imam Askari (a.s) an rufe su a gidajensu wadanda suka kasance suna ibada da zikirin Ubangiji a cikinsu. Saboda haka wadan gidaje bisa la’akari da wannan aya sun cancanci a daukaka su, sannan dole ne a kauce wa rusa su domin ya saba wa wannan aya.

A unguwar Bani Hashim a garin Madina shekaru kadan da suka gabata gidan Imam Hasan da Husain (a.s) da makaranta Imam Sadik (a.s) sun kasance a wadannan wurare, Marubucin wannan littafi shi kansa ya ziyarci wadannan wurare, amma abin bakin ciki tare da fakewa da fadada masallacin Manzo duk an rusa wadannan wurare masu dinbin tarihi da albarka. Duk da cewa ana iya yin wannan aiki na fadada masallacin Manzo (s.a.w) ba tare da rusa wadan wurare ba.

 

Soyayyar Manzo (s.a.w) Da Iyalansa

Ayoyin da hadisai da dama sun zo domin bayani a kan soyayya ga Manzo da ‘yan gidansa (a.s).

Kur’ani ya nuna mana cewa imanin mai ceto shi ne yana tare da wanda yake son Manzo da jihadi a tafarkin Allah fiye da komai a cikin zuciyarsa: “Ka ce idan iyayenku da ‘ya’yanku da matanku da ‘yan’uwanku da dukiyoyinku wadda kuka tara, da kasuwanci da kuke tsoran ku fadi a cikinsa, da gidajenku da kuke kaunarsu, idan sun kasance sun fi soyuwa a gareku daga Allah da manzonsa da jihadi a tafarkin Allah sai ku saurara har al’amarin Allah ya zo, Allah ba ya shiryar da mutane fasikai”.[16]

Ayar sama tana Magana ne a kan abubuwa guda uku wadanda mafi yawa soyayyar mutum takan ta’allaka da su, wato Iyalai da dukiya da gidaje da saye da sayarwa. Amma mumini na hakika shi ne wanda Allah da mazonsa da jihadi a tafarkin Allah ya fi soyuwa a gare shi fiye da wadancan abubuwa da aka ambata.

 Amma a wata aya ana bayani ne a kan soyayyar iyalan gidan Manzo ga abin da take cewa: “Ka ce ban nemi wani abu a kan sakon manzancin da na zo da shi ba a matsayin lada sai soyayya ga iyalan gidana”. [17]

 Sannan Manzo yana bayyana wasu abubuwa guda uku wadanda suke nuna dandana zakin imanin mutum, daya daga cikinsu shi ne soyayya ga Allah da shi manzon: Abubuwa guda uku ne duk wanda yake da su to ya dandana zakin imani, daya daga cikinsu kuwa shi ne ya kasance a wajan mutum son Allah da manzonsa ya fi komai a wajensa…



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 next