Girmama Kaburbura Masu Tsarki



4-Jalaluddin Suyudi ya ruwaito daga Anas Bn Malik Yana cewa: Yayin wannan aya wadda take cewa “A cikin gidajen da Allah ya yi Umarni da a daukaka…”. Sai ya karanta a cikin masallaci, sai wani daga cikin sahabban Manzo ya mike ya tambayi Manzo me ake nufi da wadannan gidaje?

 Sai Manzo ya amsa masa da cewa: Ana nufin gidajen Annabawa, a wannan lokaci sai Abubakar ya mike ya ce: Ya nuna gidan Ali da Fadima (a.s) ya ce: Wadannan gidajen suna cikin wadanda Allah ya yi izini da daukaka su? Sai Manzo (s.a.w). Ya amsa masa da cewa: E, suna ma daga cikin mafi daukakarsu.[8]

 Imam Bakir (a.s) yana cewa: Abin da ake nufi da gidaje a cikin wannan aya shi ne, gidajen Annabawa da gidan Ali (a.s)[9]

 Bisa dogaro da wadannan dalilai muna iya fahimtar cewa abin da ake nufi da gidaje a cikin wannan aya ta cikin Suratun Nurr shi ne gidajen annabawa da waliyyan Allah, sakamakon tasbihi da tsarkake Allah da ake yi a cikinsu yake da wani matsayi na musamman, kuma Allah ya yi izini da yin kokari wajen a daukaka su.

 5-Sannan dalili wanda yake a fili a kan cewa abin da ake nufi da gidaje a cikin wannan aya su ne, ayoyi guda biyu da suka zo kamar haka:

Allah madaukaki yana yi wa Annnabi Ibrahim da matarsa magana kamar haka:

A-”Rahmar Allah da albarkarsa ta tabbata a gare ku ya ku ma’abota gida[10].

 B-Allah Kawai ya yi nufi ya tafiyar muku da kazanta yaku Ahlul baiti, ya kuma tsarkake ku tsarkakewa.[11]

Kai ka ce wadannan gidaje su ne cibiyar hasken Ubangiji.

Tare da kula da wadannan dalilai guda biyar da muka kawo muna iya cewa: Masati da daukakar wadannan gidaje sakamakon wadanda suke zaune a cikinsu ne, suna tasbihin Ubangiji suna tsarkake shi. A hakikanin gaskiya wannan aya tana magana ne dangane da gidaje irin gidajen Annabi Ibrahim da Manzo (s.a.w), a nan kuwa sakamakon tasbihi da tsarkake Ubangiji da ake yi a cikinsu, shi ne ya sanya Allah madaukaki ya daga martaba da darajarsu.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 next