Girmama Kaburbura Masu Tsarki



 Mai yiwuwa a ce: Karkashin wannan aya ana cewa: “Yana tasbihinsa a cikinsu safiya da yamma”. Wato abin da ake nufi da “Buyut” Masallatai. Domin kuwa muslmin farkon zuwan musulunci sun kasance suna halarta sallar jam’i baki dayansu. Saboda haka tasbihi da tsarkake Ubangiji ana yin sa ne a cikin masallaci.

 Amma wannan fahimta ba dai-dai ba ce, domin kuwa ana aiwatar da sallar wajibi ne kawai a cikin masallatai, sannan mustahabbi ne a gabatar da sauran sallolin mustahabbi a cikin gidaje. Sannan ya kamata ma mutum ya kasa ibadarsa zuwa gida biyu, wato wani bangare na farilla ya aiwatar da su a cikin masallaci, sannan bangaren nafiloli ya gabatar da su a cikin gida.

Mai yiwuwa wasu suga wannan bai inganta ba, amma hakikanin al’amarin haka yake domin kuwa ruwayoyi da dama sun karfafa hakan. Muslim acikin sahih dinsa, ya kawo babi mai zaman kansa wanda yake nuna mustahabbancin sallar nafila a cikin gida. A kan haka ya ruwaito ruwayoyi da dama, amma a nan kawai zamu kawo wasu a matsayin misali:

 Manzo mai tsira da aminci yana cewa: “Fiyayyar sallar mutum a cikin gidansa, sai dai sallolin wajibi”[12].

 Wannan ruwaya tana nuna mana cewa Manzo (s.a.w) da sauran sahabbansa suna yin sallolinsu na nafila a cikin gidajensu, sakamakon haka ne gidajen annabawa da na salihan bayi suka zama wurin zikirin Allah da tsarkake shi. Sannan kuma dalilin wannan ne Allah ya ba da izini a kan daukaka su. A yanzu dole ne mu ga me ake nufi daga matsayin wadannan gidaje?

 Me ake nufi da daukaka wadannan gidaje?

A baya mun yi bayanin cewa, kafa hujja da wannan aya yana bayyanar da abubuwa guda biyu ne. Abu na farko kuwa shi ne, bayyanar da ma’anar “buyut” wanda muka yi cikakken bayaninsa a baya, yanzu lokaci ya yi da zamu yi bayani a kan abu na biyu wanda shi ne daukaka wadannan gidaje da Allah yake horo da shi.

 Hakika kalmar “Rafa’a” cikin Kur’ani tana zuwa ne da ma’anar daga gini kamar yadda ta zo a cikin wannan ayar: “Shin halittar su ita ce tafi wahala ko kuwa sama wadda ya gina ta? Sannan ya daga rufinta ya kuma daidaita ta?[13]

Amma kalmar “rafa’a” a cikin wannan aya ba yana nufi yin gini ba, domin kuwa an dauka cewa akwai gida ne, Kur’ani yana magana a kan siffofin wannan gida ne. Saboda haka abin da ake nufi da wannan kalma a cikin wannan aya shi ne daga matsayinsu da girmama su, mafi yawan masu tafisiri sun dauki wannan ma’ana duk da cewa wasu daga ciki sun tafi a kan ma’anar da muka ambata a baya.[14]

A bayyane zamu iya cewa: Wuraren da Allah yake ambatar “Buyut” yana nufin gidajen da bayin Allah suke kwana suna yin tasbihin Ubangiji kuma suna tsarkake shi. Saboda haka daukaka wadannan gidaje ba ya nufin daga gininsu ko rufinsu ba ne, abin da ake nufi shi ne daga matsayi da martabarsu. Daya daga cikin wannan girmamawa da daga matsayinsu kuwa shi ne ya zamana an tsarkake su daga dukkan wata kazamta, sannan duk inda suka dan lalace a gyara su. Dukkan wannan aiki za a yi shi ne saboda girmama wadanda suka kasance a cikin wadannan gidaje suna tasbihin Ubangiji suna salloli kuma ba su kin fitar da zakka. Domin girmama wadannan mutane ne Allah ya yi horo da a girmama wadannan gidaje, sannan a kare su daga rushewa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 next